NASU da SSANU za su yi zanga-zangar kwanaki 3 a fadin Najeriya

NASU da SSANU za su yi zanga-zangar kwanaki 3 a fadin Najeriya

Kwamitin kungiyoyin manyan ma’aikatan jami’a a Najeriya watau SSANU, da kuma kungiyar kananan Ma’aikata na NASU wanda ba su shiga aji, su na barazanar shiga yajin aiki a Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto mana cewa kungiyoyin SSANU da NASU za su sake shiga wani sabon yajin aiki idan har gwamnati ba ta yi komai a game da tsarin rabon kudin da a ka fitar ba.

Kungiyoyin ma’aikatan jami’an kasar sun nuna rashin jituwarsu a game da yadda Malaman makaranta da ke karkashin kungiyar ASUU za su tashi da 80% na kudin da gwamnati ta fitar.

Kwanan nan ne gwamnatin tarayya ta warewa ma’aikatan jami’o’i Naira biliyan 25; wanda ASUU ke neman lashe kashi 4 cikin 5 na wannan kudi. A dalilin haka ne SSANU da NASU za su yi bore.

KU KARANTA: Gwamnati ta nemi binciki mutuwar wani Dalibin Najeriya a waje

Wannan labari ya zo mana ne a Ranar Lahadi, 14 ga Watan Yuni, 2019. Hakan na nufin idan gwamnati ba ta dauki mataki ba, gobe za a tashi da zanga-zanga na kwana uku a fadin kasar.

Shugaban kwamitin wadannan kungiyoyi, Kwamred Sampson Ugokwe, ya fadawa Manema labarai cewa ba za su yi na’am da yadda ma’aikatar ilmi ta kasa alawus din jami’o’in kasar ba.

Sampson Ugokwe ya nuna cewa SSANU da NASU kadai su na bukatar Naira biliyan 30 a matsayin alawus din karin aikin da su ka yi daga 2009 zuwa 2016 tare da albashin wasu da a ka tsaida.

Bayan nan kuma kungiyoyin sun ce ba su yarda da sabon tsarin fanshon da a ka kawowa jami’o’i ba inda a ka wakilta Malaman jami’a na ASUU a matsayin shugaban kamfanin nan NUPENCO.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel