Ina da shanu sama da 100, ni ma na can-can-ci a bani Ruga, cewar Dino Melaye

Ina da shanu sama da 100, ni ma na can-can-ci a bani Ruga, cewar Dino Melaye

-Sanata Dilo Melaye, mai wakiltar Kogi ta yamma, ya bayyana a cikin raha cewa shi ma ya zama dan kugiyar Miyetti Allah

-Melaye ya bayyana haka ne a wajen taron rufe mahaifiyarshi, Comfort Melaye a garin Aiyetoro-Gbedde dake a karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi

-Ya bayyana cewa ya samu shanu 104 daga wajen masu yi mashi jaje sakamakon rasuwar mahaifiyarshi, a saboda haka zai tambayi shugaba Buhari ya sama mashi Ruga

A ranar Asabar 13 ga watan Yuli 2019, sanata Dilo Melaye, mai wakiltar Kogi ta yamma, ya bayyana a cikin raha cewa shi ma ya zama dan kugiyar Miyetti Allah sa’annan ya kara da cewa ya kamata shi ma a sama mashi wajen zama na Ruga.

Ya bayyana cewa ya samu shanu 104 daga wajen masu yi mashi jaje sakamakon rasuwar mahaifiyarshi, Deaconess Comfort Melaye, a sabida haka ya cancanci zama dan kungiyar Miyetti Allah.

Melaye ya bayyana haka ne a wajen taron rufe mahaifiyarshi, Comfort Melaye a garin Aiyetoro-Gbedde dake a karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi. Ta mutu tana da shekaru 70.

Manyan mutane da suka halarci taron da aka gudanar a cocin Apostolic dake a Oke-Ayo, Iluafon, sun hada da wakilin shugaban kasa kuma mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar dattawa, sanata Ita Enang, wanda ya mika takardar ta’aziyyar shugaba Buhari, da kuma wakilin babban hafusun sojin kasa ta Najeriya.

Saura sun hada tsohon shugaban majalisar dattawa sanata Bukola Saraki, sanata Ike Ekweremadu, tsohon kakakin majalisar wakila, Dimeji Bankole, sanata Ifeanyi Uba, sanata Ita Giwa da dai sauransu.

Da yake mika sakon godiyarshi ga daukacin yan Najeriya, musamman babban hafsun sojin kasa, janar Tukur Burutai, wanda ya bayyana cewa ya tsaya tare da shi a lokacin da yake jimamin rashin mahaifiyarshi, Melaye ya tabo maganar dakatar da Ruga a fakaice.

KARANTA WANNAN: Wasu Gwamnonin da su ka sauka daga mulki su na neman kujerun Minista

Melaye ya bayyana cewa, tunda yanzu ya na da shanu sama da 100 ya zama “Dan kungiyar Miyetti Allah yanzu” kuma ya dace a ce an bashi wajen zama na Ruga.

Da yake godewa daukacin yan Najeriya akan jajenta mashi da sukayi na rashi mahaifiya, Melaye ya bayyana cewa “Tsawon lokacin nan na samu shanu 104, saboda haka yanzu zan iya cewa ni ma dan kungiyar Miyetti Allah ne, saboda haka zan tambayi shugaba Buhari ya sama mani Ruga.”

Sanata Melaye ya bayyana kyautar Naira miliyan biyar ga cocin Apostolic bayan Naira miliyan daya da jam’iyyar PDP ta bayar.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel