A binciki abin da ya kashe Orhions Ewansiha – Inji Abike Dabiri

A binciki abin da ya kashe Orhions Ewansiha – Inji Abike Dabiri

Shugabar hukumar ‘Yan Najeriya da ke zaune a kasahen waje, NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa, ta nemi a gudanar da bincike a game da mutuwar wani ‘Dan Najeriya Thomas Orhions Ewansiha.

Misis Dabiri-Erewa ta nemi ofishin Jakadancin Najeriya da ke babban Birnin Kuala Lampur na kasar Malayisa inda abin ya auku, su yi bincike domin gano abin da ya kashe Orhions Ewansiha.

Kafin rasuwarsa, wannan Bawan Allah daga Najeriya Marigayi Thomas Orhions Ewansiha ya kasance ‘Dalibin da ke karatun Digirinsa na uku watau PhD a jami’ar Limkokwing da ke Malaysia.

KU KARANTA: Amurka ta gargadi Mutanenta su guji wuraren taron ‘yan shi’a a Najeriya

A jawabin na ta, Abike Dabiri-Erewa ta kuma nuna cewa ya kamata gwamnatin Najeriya ta tabbatar wajen ganin mutanen kasar ta da ke waje ba su fama da wata matsalar rashin jin dadi.

Shugabar NIDCOM ta yi wannan jawabi ne da bakinta inda ta nuna takaici da jimamin wannan rashi. Abike Dabiri ta ce Ewansiha ya na da takardu amma jami’an Malaysia su ka garkamesa.

Bayan an daure wannan Bawan Allah na tsawon kwanaki 14 ne ya yanke jiki ya fadi. Abike Dabiri ta yi wa Iyalin mamacin ta’aziyya tare da addu’ar hakurin jure wannan mummunan rashi.

Orhions Ewansiha ya na karatu ne a jami’ar fasahar nan ta Limkokwing ne da ke cikin Garin Selangor a Malaysia inda ya mutu ya bar Iyali a gida; Matarsa guda da kuma ‘Ya ‘ya har biyu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel