Wasu Gwamnonin da su ka sauka daga mulki su na neman kujerun Minista

Wasu Gwamnonin da su ka sauka daga mulki su na neman kujerun Minista

Wasu daga cikin tsofaffin gwamnoni su na cikin wadanda ke neman samun wuri a cikin sabuwar gwamnatin Buhari kamar yadda shugaban kasar ya tabbatar da cewa an huro masa wuta a yanzu.

Wani bincike da Jaridar The Nation ta yi, ya nuna cewa Gwamnonin da su ka bar gadon-mulki a Najeriya su na neman kujerun Minista ko kuma akalla su zakulo wadanda za a nada a jihohinsu.

Sai dai duk yadda wadannan tsofaffin gwamnoni su ka kwallafa rai a mukaman Ministocin kasar, irin badakalar da su ka tafka lokacin su na ofis zai yi wahala ya sa hakar ta su ta cin ma ruwa.

Rahotanni na yawo cewa wani daga cikin tsofaffin gwamnonin ya na raba Dalolin kudi domin ganin ya samu kujerar Minista. Wannan ne ya sa shugaban kasar ya shiga cikin mawuyacin hali.

KU KARANTA: An soma gogawa Tinubu da Osinbajo bakin jini saboda 2023

Yayin da gwamnonin da su ka sauka daga mulki su ke harin Minista ido rufe, gwamnoni masu-ci sun dage wajen ganin su ne su ka kawowa Buhari sunayen wanda zai nada a jihohin na su.

Gwamnonin da su ka sauka daga mulki su na neman zama Ministoci ne domin gudun siyasar jihohinsu ta kubuce masu. A na su lissafin, idan su ka zama Ministoci, za a cigaba da damawa da su.

Wannan ya sa ‘yan siyasar ke kokarin ganin Buhari bai zakulo wani na-dabam ya ba wannan mukami ba, domin hakan ya na iya jawo su rasa tasirin su a jihar a hannun sabon Ministan.

Haka zalika wasu tsofaffin gwamnonin su na harin kujerun Minista ne domin hana gwamnati ta binciki barnar da su ka yi a baya. Yanzu dai babu wanda ya san inda shugaban kasar ya sa kai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel