Olakunrin: Ya kamata Shugaba Buhari ya kawo karshen kashe-kashe a Najeriya - PDP

Olakunrin: Ya kamata Shugaba Buhari ya kawo karshen kashe-kashe a Najeriya - PDP

Mun ji cewa babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya watau PDP ta fito ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi maganin irin munanan kashe-kashen da a ke yi cikin kasar nan.

Jam’iyyar adawar ta koka da kisan gillaar da a ka yi wa ‘Diyar babban jagoran nan na kungiyar kasar Yarbawa ta Afenifere watau Funke Olakunrin inda tace wannan abu da matukar cin rai.

A cewar Sakataren yada labarai na PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, gwamnatin kasar ta ki maida hankali yadda ya dace wajen gano wadanda su ka kashe wannan Baiwar Allah Funke Olakunrin.

“Jam’iyyar mu ta damu da yadda jami’an tsaro su ka karkata da muhawara a kan fuskar wadanda su ka yi wannan kisa tare da kawo maganar sace Marigayiyar kafi a soma binciken mutuwarta” Inji Kola Ologbondiyan.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane su ka kashe Funke Olakunrin - 'Yan Sanda

Kakakin na PDP ya cigaba da cewa:

“Kisan Olakunrin ya shiga cikin sahun rashin da a ka yi a dalilin sakacin gwamnatin Buhari na kare rayukan al’umma da gaske.

Kola Ologbondiyan ya ce: "Abin ya wuce gwamnati ta rika ta’aziyya daga Abuja.”

Don haka ne Mai magana a madadin PDP din ya ce ba za su bari wannan kisa ya wuce haka nan ba, dole Sufetan ‘Yan Sanda ya cafko wadanda su ka yi wannan aiki cikin gaggawa a hukuntasu.

PDP ta na ganin duk abin da Buhari ya ke fada zakin-baki ne kurum da bai wuce fatar-baki ba, a dalilin wannan ta nemi shugaban ‘yan sandan kasar Mohammed Adamu ya dage da bincike.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel