Yadda muka hana a tsige Obasanjo - Yakubu Gowon

Yadda muka hana a tsige Obasanjo - Yakubu Gowon

- Tsohon shugban kasa, Yakubu Gowon ya ce shi da wasu manyan 'yan Najeriya ne suka sanya baki suka hana a tsige Olusegun Obasanjo daga mulki

- Gowon ya ce wasu daga cikin manyan 'yan Najeriya da suka taka rawa wurin hana tsige Obasanjo sun hada da Abdulsalami Abubakar da tsohon shugaban kasa Ernest Shonikan

- Tsohon shugaban ya ce da an bari majalisa ta kunyata Obasanjo ta hanyar tsige shi, wadanda za su biyo bayan sa ma hakan na iya faruwa da su

Tsohon shugban kasa, Janar Yakubu Gowon (murabus) ya ce shi da wasu manyan 'yan Najeriya ne suka roki tsohon Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya, Ghali Umar Na'Abba da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Pius Anyim kada su tsige Olusegun Obasanjo yayin da ya ke shugaban kasa.

Gowon ya bayyana hakan ne a ranar Asabar 13 ga watan Yuli, yayin da ya ke jawabi wurin lakca da aka shirya na karrama marigayi Manja Janar Emmanuel Olumuyiwa Abisoye a Abuja kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Mutum 5 da suka mallaki arzikin da ya fi kasafin kudin Najeriya

Gowon ne babban bako a wurin taron kuma Ghali Na'Abbah shima yana daga cikin manyan bakin da aka gayyata.

Tsohon shugaban kasar ya ce shi da Abdulsalami Abubakar da tsohon shugaban kasa Ernest Shonikan da wasu manyan 'yan Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wurin hana shugabanin Majalisar Tarayyar na wancan lokacin tsige Shugaba Obasanjo.

"Na ga Alhaji Ghali Na'Abbah yana nan kuma ina tabbatar muku da cewa munyi tattaunawa wasu batutuwa masu muhimmanci kuma na san cewa sai da muka roke shi da tsohon shugaban majalisar dattawa kada su tsige Obasanjo kuma suka saurare mu saboda suna ganin girman mu," inji shi.

"Idan da mun bari sun tsige shugaban kasar a lokacin da demokrayar mu ke jinjira da babu wani shugaban kasa a Najeriya da hakan ba za ta iya furuwa da shi ba. Saboda haka na bisa sauraron mu da kayi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel