Muna samun nasara a yaki da 'yan ta'adda - Buhari

Muna samun nasara a yaki da 'yan ta'adda - Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce Rundunar Sojojin Najeriya da abokan aikinsu suna samun nasara a yakin da su keyi da 'yan ta'adda.

Shugaban ya yi wannan furucin ne wurin bikin yaye manyan hafsoshin sojoji karo na 41 da aka gudanar a Jaji a jihar Kaduna a ranar Asabar.

Ya yabawa hadin gwiwa da Najeriya ke yi da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita wurin yaki da 'yan kungiyar Boko Haram inda ya ce kwalliya tana biyan kudin sabulu.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Mutum 5 da suka mallaki arzikin da ya fi kasafin kudin Najeriya

"Mafi yawan barazanar da Najeriya ke fuskanta daga kasahen waje ne. Hakan yasa dole yankin Afirika Ta Kudu ta kara zage damtse wurin hadin gwiwa tsakanin sojoji a tsakaninsu.

"Na san kun san hadin gwiwan da Najeriya tayi da Kamaru da Nijar da Benin da Chadi domin yakar Boko Haram a Tafkin Chadi da ma wasu wurare.

"Hadin gwiwar yana haifar da sakamako mai kyau, ana samun nasarar yaki da 'yan ta'addan a dukkan kasashen.

"Ina son tabbatar muku da cewa Najeriya da abokan huldar ta ba za suyi kasa a gwiwa ba har sai mun ga bayan 'yan ta'addan," inji shi.

Shugaban kasar ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta cigaba da bayar da muhimmanci kan walwala da jin dadin sojoji da makarantun bayar da horon sojojin.

Ya kuma yi amfani da damar wurin mika godiyarsa ga Dakarun Sojojin Kasar bisa gaggawar kai dauki da suke yi a duk lokacin da kasar ke fuskantar kallubalen tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel