Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Hatsarin mota ya hallaka mutane 5 tare da jikkata 14

Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Hatsarin mota ya hallaka mutane 5 tare da jikkata 14

Wani hatsari a tsakanin wata motar bus da babbar mota yayi sanadiyar mutuwar mutane biyar yayinda wasu 14 suka jikkata a hanyar babban titin Abeokuta – Ibadan.

Kwamandan hukumar da ke kula da afkuwar hatsarurruka (FRSC), Clement Oladele, a ranar Asabar, 13 ga watan Yuli ya bayyana cewa hatsarinya afku ne yankin Odeda da ke babban titin.

Oladele ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne a tsakanin wata motar bus kirar MAZDA me lamba MUS367XU, dauke da fasinjoji da kuma wata babbar motar Iveco mara lamba.

“Abunda ake zargin ya haddasa hatsarin shine tukin ganganci. Babbar motar ta murkushe fasinjojin da ke cikin bus din sannan ta garkame su a cikin bus din,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya amince ayi wa manyan jami’ai 10 karin girma a karkashin ma’aikatar cikin gida (cikakken sunaye)

Yace an dauki gawawwakin zuwa dakin ajiye gawa na babbar asibitin Ijaye da ke Abeokuta, yayinda wadanda suka jikkata ke jinya a cibiyar kiwon lafiya na tarayya da ke Abeokuta.

Kwamandan ya gargadi direbobi akan su guje ma tukin ganganci don guje ma hatsari mara amfani sannan ya bukaci fasinjoji da jama’a baki daya da suka kai rahoton direbobi masu tukin gangaci ga hukumar FRSC ta hanyar kiran lamba 112.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel