Obasanjo yayi Allah wadai da kisan ‘Yar shugaban kungiyar Yarabawa

Obasanjo yayi Allah wadai da kisan ‘Yar shugaban kungiyar Yarabawa

- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya aika sakon ta’aziyya ga iyaalan shugaban kungiyar Yarbawa, Rueben Fasoranti kan rasuwar ‘yarsa

- Masu garkuwa da mutane ne suka kashe yarinyar shugaban kungiyar na Afenifere

- Obasanjo ya kuma yi kira ga gwamnatoci da na tarayya da su mayar da hankali wajen ganin an kawo karshen hare-haren makiyaya

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya aika sakon ta’aziyya da jaje ga iyalan shugaban kungiyar Yarbawa ta Afenifere, Rueben Fasoranti kan rasuwar ‘yarsa da masu garkuwa da mutane suka kashe.

Obasanjo ya yi addu’ar Allah ya ji kanta sannan kuma ya ba iyayenta da ‘yan uwa juriyar wannan rashi da sukayi.

Hakazalika tsohon Shugaban kasar ya yi kira ga gwamnatoci da na tarayya da su mayar da hankali wajen ganin an kawo karshen hare-haren makiyaya da ya addabi kasar nan.

Obasanjo ya aika da sakon ne ta hannun tsohon gwamna Yerima Oyinlola Ogunseye, kafin har ya dawo daga kasar Morocco.

A halin da ake ciki mun ji cewa Aare Onakakanfo na kasar Yarabawa, Cif Gani Adams ya ce yarabawa za su dauki mataki kan kisar gillan da aka yi wa diyar shugaban kungiyar Afenifere.

Ya ce kada wanda ya ga laifin kungiyar idan wani abu ya faru. 'Yan bindiga sun harbe diyar Reuben Fasoranti, Funke Olakunrin ne a ranar Juma'a a hanyar Kajola zuwa Ore a jihar Ondo.

KU KARANTA KUMA: Magana ta kare: Hukumar 'Yan sanda ta bayyana yadda masu garkuwa da mutane suka kashe 'yar shugaban Afenifere

'Yan sanda sun ce masu garkuwa da mutane ne suka kashe ta amma kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta ce makiyaya ne suka kashe ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel