Fashi da makami: Jerin sunayen sojoji 5 da ake nema ruwa a jallo

Fashi da makami: Jerin sunayen sojoji 5 da ake nema ruwa a jallo

Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da cewa tana neman wasu dakarunta biyar ruwa a jallo saboda yi wa wani babban mutum fashi da makami.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa sojojin sun hada da

1- Cpl Gabriel Oluwaniyi

2 - Cpl Mohammed Aminu

3 - LCpl Commander Haruna

4 - LCpl Oluji Joshua

5 - LCpl Hayatudeen.

A cewar rahoton, sojojin suna cikin wadanda ke aiki a karkashin atisayen operation Harbin Kunama III da ke Sokoto kuma an tura su rakiya ne daga Sokoto zuwa Kaduna misalin karfe 3 na ranar Juma'a.

DUBA WANNAN: Za a biya tsohon gwamnan PDP da ke gidan yari N151.1 a matsayin kudin fansho

"Babban mutumin yana cikin farar Hilux ne yayin da sojojin kuma ke cikin motar mai dauke da bindiga. Sojojin sun hada baki ne suka yi wa babban mutumin fashi.

"Sai dai sojojin sun bar motarsu a filin saukan da jirage ke sauka a Jaji. Sun kuma tarwatse inda kowa ya kama hanyarsa kamar yadda na'urar gano inda mutane suke ya nuna cewa wasu sun nufi Jos, Suleja da sauransu," kamar yadda rahoton ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel