Kisar diyar Fasoranti: Kada a ga laifin mu idan muka dauki mataki - Gani Adams

Kisar diyar Fasoranti: Kada a ga laifin mu idan muka dauki mataki - Gani Adams

Aare Onakakanfo na kasar Yarabawa, Cif Gani Adams ya ce yarabawa za su dauki mataki kan kisar gillan da aka yi wa diyar shugaban kungiyar Afenifere.

Ya ce kada wanda ya ga laifin kungiyar idan wani abu ya faru.

'Yan bindiga sun harbe diyar Reuben Fasoranti, Funke Olakunrin ne a ranar Juma'a a hanyar Kajola zuwa Ore a jihar Ondo.

'Yan sanda sun ce masu garkuwa da mutane ne suka kashe ta amma kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta ce makiyaya Fulani ne suka kashe ta.

Cikin 'yan kwanakin nan ana ta dora alhakin fashi da makami da garkuwa da mutane da ake yi kan makiyaya.

DUBA WANNAN: Jonathan ya roki wata alfarma ta musamman a wurin gwamnatin Buhari

Manyan 'yan siyasan Najeriya ciki har da Shugba Muhammadu Buhari da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da mataimakinsa Atiku Abubakar sunyi Allah wadai da kisar.

Mutane da dama suna ta aike wa da sakon ta'aziyya ga Mr Fasoranti mai shekaru 94 tun bayan da aka sanar da afkuwar harin.

Mista Adams, shugaban kungiyar Oodua Peoples Congress, wacce a baya kungiyar masu tayar da kayan baya ne a kudu maso yamma ya ce 'abin ya yi yawa' yayin da ya ke magana kan kisar Olakunrin.

A jawabin da mai taimaka masa kan kafafen sadarwa, Kehinde Aderemi ya fitar, Adams ya ce Yarabawa ba su rasa abinda za suyi ba domin kawo karshen ta'addancin da makiyaya Fulani ke yi amma sun cigaba da sanar da duniya abinda ke faruwa.

Adams ya ce "Muna son duniya ta zama shaida kan abinda ake yi wa mutanen mu,"

"Su sani cewa akwai abinda zai biyo baya kan wannan abinda suka aikata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel