Na san ‘yan siyasan da suka zama biloniyoyi a dare daya – Amaechi

Na san ‘yan siyasan da suka zama biloniyoyi a dare daya – Amaechi

-Tsohon ministan sufuri ya zaburar da wasu matasa masu sha'awar zama shugabanni a jihar Legas inda ya sanar da su kalubalen dake gabansu

-Amaechi a cikin jawabinsa ya fadi cewa ya san 'yan siyasan da suka zama biloniyoyi a dare guda alhalin kuma dukiyar al'ummace suka handame

-A watan Janairun da ya gabata an samu wani faifan odiyo wanda Amaechin ke cewa 'qasar Najeriya ba inda za ta domin ba ta da alqibla'

Tsohon ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi ya fadi cewa akwai ‘yan siyasan da suka zama biloniyoyi a yanzu alhalin da can ba haka suke ba.

Amaechi yayi wannan furucin ne a wurin wani taron ganawa da aka shirya domin zaburar da matasa masu sha’awar shugabanci a jihar Legas ranar Juma’a.

KU KARANTA:Amurka ta gargadi yan kasarta mazauna Najeriya da su guji wuraren da ‘yan shi’a ke taruwa

Tsohon ministan har ila yau, ya yi kira ga ‘yan siyasa da su duqufa wurin yin ayyukan cigaban kasa da kuma samar da abubuwan yi wanda zai rage aukuwar ta’addanci a kasar.

Kamar yadda tsohon ministan ya fadi: “ Na san ‘yan siyasan da suka zama biloniyoyi a dare guda. Kuma kowa ya san wannan kudade ne da ya kamata a ce anyi amfani da su wurin bunqasa rayuwar talaka.

“ Ya kamata ‘yan siyasarmu su rika fitowa fili suna sanar da mutane irin taimakon da suke iya yi masu wanda zai tsamo su daga qangin talauci.”

A wani sako da aka samu mai dauke da muryar Amaechi a watan Janairu, an same shi yana fadin cewa hanya daya da za’a bi wurin gyaran kasar nan ita ce “a kashe kowa.”

“ Babu inda kasar nan zata, lokacin da Magnus Abe ke sakataren gwamnatin jihar Rivers, na taba fada mashi cewa wannan kasar ta mu ba ta da alqiba, yace dani yallabai ka bar fadin haka, wannan magana ba ta kamace ka ba a matsayinka na Gwamna.

“ Bayan wata biyu kacal Abuja, sai Magnus ya zo ya same ni yake cewa yallabai ka yi gaskiya kasar nan ba ta da alqibla. Babu abinda akeyi a Abuja sai raba kudin kasa.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel