Magana ta kare: Hukumar 'Yan sanda ta bayyana yadda masu garkuwa da mutane suka kashe 'yar shugaban Afenifere

Magana ta kare: Hukumar 'Yan sanda ta bayyana yadda masu garkuwa da mutane suka kashe 'yar shugaban Afenifere

- An fara bayyana yadda aka kashe 'yar gidan shugaban yarabawa Afenifere, Reuben Fasoranti

- Legit.ng ta kawo muku rahoton cewar an harbe Funke Olakunrin akan babbar hanyar Benin zuwa Ore

- Mai magana da yawun Afenifere, Yinka Odumakin, ranar 12 ga watan Yuli ya dora alhakin kisan akan makiyaya

Rundunar 'yan sandan jihar Ondo, ta bakin mai magana da yawunta, Femi Joseph, yau Asabar dinnan 13 ga watan Yuli, ya bayyana yadda aka harbe Funke Olakunrin, 'yar gidan shugaban Afenifere,Reuben Fasoranti, wacce masu garkuwa da mutane suka harbe ranar 12 ga watan Yuli.

Da yake gabatar da wannan mummunan labari ga manema labarai, Joseph ya bayyana cewa bashi da masaniya cewa Funke 'yar gidan Fasoranti ce.

A rahoton da ya bayar akan kisan Funke, kakakin rundunar ya bayyana cewa: "Lamarin ya faru a tsakanin Kajola da Ore, a lokacin da 'yan ta'addar kusan su 15, suka budewa wasu motoci guda biyu masu kirar Toyota Land Cruiser da kuma Toyota Camry.

KU KARANTA: El-Rufai: 'Yan majalisa sun yi daidai da suka ki bawa mai zagina kujerar kwamishina

"Land Cruiser din tana dauke da fasinja guda biyar, ciki hadda marigayiyar, wacce daga baya muka gano cewa Funke ce. Bayan sun harbe ta munyi gaggawar kai ta asbiti, amma rai yayi halinsa.

"Sauran mutane hudu da suka yi garkuwa dasu mun kwato su. Mutane uku na cikin Camry ma suma sunyi garkuwa da su amma mun kwato su. Mun ceto rayukan mutane bakwai wadanda suka dauka lokacin da suka kai harin.

"Har yanzu akwai sauran mutum daya da ya rage wanda bamu gani ba, kuma muna yi iya bakin kokarin mu don ganin an hukunta wadannan 'yan ta'adda."

Joseph kuma yayi watsi da zargin da kakakin Afenifere yake yi na cewa makiyaya ne suka kashe Funke. Kakakin rundunar 'yan sandan yace har sai an kama masu laifin sannan za a iya tabbatar da wane irin yare ne su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel