Buhari ya amince ayi wa manyan jami’ai 10 karin girma a karkashin ma’aikatar cikin gida (cikakken sunaye)

Buhari ya amince ayi wa manyan jami’ai 10 karin girma a karkashin ma’aikatar cikin gida (cikakken sunaye)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kara wa manyan jami’ai goma a hukumomin tsaro da ke karkashin ma’aikatar cikin gida.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa hukumomin Civil Defence, na kashe gobara, da kuma hukumar fursuna sun saki sunaye jami’ai 10 da aka yiwa Karin girma daga matsayin mataimakin kwanturola/ Kwamanda da Kwanturola – Janar (ACGs) zuwa matsayin mataimakin kwanturola/ kwamanda da kuma Kwanturola- Janar (DCGs) a fadin hukumomin hudu.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: Da wuya Najeriya ta kai 2023 – Inji tsohon dan takarar shugaban kasa

Jerin sunayen jami’an da aka kara wa matsayi daga mukamin ACGs zuwa mukamin DCGs sune:

A. Hukumar kashe gobara

1. Azogu, Gerald Imo

B. Hukumar Fursuna na Najeriya

1. Bitrus, Filibus Ndirmbula Borno

2. Aremu, Tajudeen O. Oyo

3. Mrabure, John O. Delta

C. Hukumar Civil Defence

1. Adamu, Soja Sabbas Yobe

2. Aminu, Kofarsoro Abdullahi Katsina

D. Hukumar kula da shige da fice na Najeriya

1. Ogwu, Julius Adadu Benue

2. Uebari, Saro John Rivers

3. Idris, Isah Jere Kaduna

4. Didi, Adaeze C. Rivers

Sakatariyar din-din-din ta ma’aikatar cikin gida, Barista Georgina Ekeoma Ehuriah, MON ta bukaci jami’an da aka yi wa Karin girma a su tabbatar da inganta tsaro da kuma yin aiki daidai da tsarin gwamnatin shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel