Aikin Hajji: Kasar Saudiyya ta karbi bakuncin mahajjatan Najeriya sama da 2000

Aikin Hajji: Kasar Saudiyya ta karbi bakuncin mahajjatan Najeriya sama da 2000

- Mahajjatan Najeriya sun isa kasar Saudiyya don aikin Hajjin 2019

- Jagoran kasar a Madinah, Alhaji Ahmad Maigari ne ya tabbatar da hakan a ranar Asabar, 13 ga watan Yuli

- Maigari ya bayyana cewa mahajjatan sun zo a jirage uku daga jihohin Lagas, Katsina da kuma Kano

Jagoran mahajjata a Madina, Alhaji Ahmad Maigari, wanda ya kuma kasance mukaddashin sakataren kungiyar da ke kula da alhazan Najeriya (NAHCON) a ranar Asabar, 13 ga watan Yuli, ya tabbatar da cewa mahajjatan Najeriya 2139 sun isa kasar Saudiyya domin aikin Hajjin 2019.

Da yake Magana da manema labarai a ranar Asabar, Alhaji Maigari ya bayyana cewa mahajjatan sun isa kasar a jirage uku daga jihohin Lagas, Katsina da kuma Kano, inda ya kara da cewa an ba mahajjatan masauki a Markassiya, kusa da Masallacin manzan Allah a Madinah, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A kokarin ganin an hana lamarin damfara, hukumar kula da jindadin alhazai na jihohi, a cewar Maigari, sun wayar da kan Musulmai akan su ziyarci wuraren yan chanji masu rijista kadai maimakon chanjin kudi a kasuwar bayan fage.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: Da wuya Najeriya ta kai 2023 – Inji tsohon dan takarar shugaban kasa

A baya Legit.ngta rahoto cewa a jiya Juma'a 12 ga watan Yuli 2019, gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya nada tsohon gwamnan jihar, Alhaji Sa'idu Dakingari a matsayin Amirul Hajji kuma shugaban wakilan alhazzai na jihar Kebbi a Hajjin 2019.

A jawabin da babban sakataren yada labarai na gidan gwamnati, Abubakar Dakingari ya fitar, an bayyana babban sakataren gidan gwamnati a matsayin sakataren wakilan.

A jawabin, an zayyana sauran wakilan da suka hada da tsohon ministan wasanni da harkokin kasashen waje Dr. Sa'idu Sambawa, tsohon ministan kimiyya da fasaha Farfesa Abubakar Ka'oje da tsohon ministan wasanni Alhaji Bala Bawa Ka'oje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel