Tirkashi: Da wuya Najeriya ta kai 2023 – Inji tsohon dan takarar shugaban kasa

Tirkashi: Da wuya Najeriya ta kai 2023 – Inji tsohon dan takarar shugaban kasa

- Fitaccen dan siyasa, Dr Uma Eleazu, ya bayyana cewa da wuya a samu Najeriya a 2023

- Dan takarar Shugaban kasar a zaben 1993 ya bayyana cewa kasar Najeriya na hawa turbar hatsari kadan-kadan

- Eleazu ya kasance mamba a kwamitin da ta shirya kundin tsarin mulkin 1999

Wani tsohon dan takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a 1993, Dr Uma Eleazu, yace ba lallai ne Najeriya ta kai 2023 ba.

Eleazu wanda ya kasance mamba a kwamitin da ta shirya kundin tsarin mulki na 1999 sannan kuma a 2006, yayi aiki a kwamitin da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kafa domin duba kundin tsarin mulki, ya bayyana cewa jumhuriya ta gaskiya ce kadai za ta ceci kasar.

Da yake Magana da jaridar Daily Sun, kwararren dan siyasar ya bayyana cewa Najeriya na kan turba mai hatsari.

Yace duba ga abunda ke faruwa a kasar yanzu, toh babu shakka mai yiwuwa mutanen kasar su tsini kansu a wani yanayi kafin 2023.

KU KARANTA KUMA: Adams Oshiomhole ne ya koya mun yadda ake fada da ubangida – Gwamna Obaseki

Yace a yanzu mutum baya iya tafiya daga kudu zuwa gabas cikin kwanciyar hankali saboda yadda ake kashe-kashe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel