Hukumar NSCDC za ta rarraba jami’anta don samar da tsaro a gonaki

Hukumar NSCDC za ta rarraba jami’anta don samar da tsaro a gonaki

-Hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) za ta rarraba karin jami’ai 1500 zuwa gonaki don samar da tsaro ga monama a kakar noman bana

-Babban kwamandan rundunar, Abdullahi Muhammadu ne ya bayyana haka a wata zantawa da yayi da kanfanin dillancin labarai na Najeriya

-Tun farkon wannan shekarar, rundunar ta rarraba kusan jami’ai 2,500 don su magance matsalar fada tsakanin makiyaya da manoma

Hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) ta ce ta kammala shirye shirye don rarraba karin jami’ai 1500 zuwa gonaki don samar da tsaro ga monama a kakar noman bana.

Babban kwamandan rundunar, Abdullahi Muhammadu ne ya bayyana haka a wata zantawa da yayi da kanfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) yau Asabar 13 ga watan Yuli 2019 a garin Maiduguri na jihar Borno.

Babban kwamandan ya bayyana cewa an dauki matakin ne don a kare manoma daga hare haren “Yan bindiga da masu garkuwa da mutane” don su samu su yi noma ba tare da wata fargaba ba.

Muhammdu ya bayyana cewa jami’ai 750 za su samu horo na sati biyar kamin a rarraba su a wurare guda takwas da suke fama matsalolin yan ta’adda a jihar Katsina.

Ya bayyana cewa jami’an za su samu horo akan yadda ake bada taimakon gaggawa, dubarun yaki, da kuma yadda ake gano bam da yadda ake cire shi, da sauran matakan samar da tsaro a cikin gida.

KARANTA WANNAN: Dalibai 11 na jami’ar Unilorin sun suma a dakin jarabawa

Ya bayyana rashin jin dadin shi game da rahotanni dake yawo cewa yan ta’adda sun hallaka manoma da yawa a cikin gonakinsu, wasu kuma da yawa an tarwatsa su sakamakon hare haren.

Muhammdu ya bayyana cewa rundunar ta kirkiri shirin samar da tsaron gonaki bayan da ma’aikatar noma ta gwamnatin tarayya ta bukace su da su taimaka wajen bayar da tsaro a wajajen kiwo 250 a fadin kasar nan.

A cikin watan Janairun wannan shekarar, rundunar ta rarraba kusan jami’ai 2,500 don su magance matsalar fada tsakanin makiyaya da manoma.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel