Amurka ta gargadi yan kasarta mazauna Najeriya da su guji wuraren da ‘yan shi’a ke taruwa

Amurka ta gargadi yan kasarta mazauna Najeriya da su guji wuraren da ‘yan shi’a ke taruwa

-Ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ya fitar da takardar gargadi ga yan asalin kasar mazauna Najeriya kan zanga-zangar da yan shi'a suka shirya gudanarwa

-Zanga-zangar da kungiyar ta yi a ranar 9 ga watan Yuli ta rikide ne zuwa fada inda har aka rashi rayukan wadansu jami'an tsaro

-Kasar Amurka ta ce idan har ya zama wajibi sai yan kasar nasu sun fita to su fita da katin wurin aiki da kuma takardar biza

Biyo bayan jerin gwanon zanga-zangar kungiyar shi’a a Najeriya da su kayi ta faruwa a ‘yan kwanakin nan, kasar Amurka ta shawarci ‘yan kasarta mazauna Najeriya cewa su kiyayi dandazo da kuma taron zanga-zangar kungiyar shi’a.

Wannan bayanin na kunshe cikin wata takarda da kasar Amurkan ta fitar a ranar Juma’a domin janyo hankalin mutanensu a kan zanga-zangar da ‘yan shi’an suka shirya gudanarwa a fadin Najeriya.

KU KARANTA:‘Yan barandan Jihar Zamfara sun tuba, sun mika makamansu ga ‘yan sanda

A dalilin hakan ne ya sanya kasar ke kira ga mutanensu kan cewa su sa ido sosai, musamman yayin zirga-zirgarsu ta wadannan ranakun.

Ga abinda takardar ke fadi: “ Ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya na kira ga ‘yan asalin kasar Amurka dake Najeriya kan zanga-zangar da kungiyar shi’a ta shirya gudanarwa cikin ‘yan kwanakin nan a fadin kasar ciki hadda Abuja da Legas.

“ Zanga-zangar wannan kungiya ta shi’a a ranar 9 ga watan Yuli ta rikide zuwa fada inda har aka yita musayar wuta a tsakanin ‘yan shi’an da ‘yan sanda wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar wasu tsirarun mutane. A don haka ofishin jakadancin Amurka a Najeriya na kira ga ‘yan asalin kasar da su guji kusantar wuraren da ake yin wannan zanga-zanga.”

Har ila yau, Amurka ta sake yin kira ga ‘yan kasarta cewa su guji duk wani wurin da jama’a ke taruwa, sannan idan har ta kama sai sun fita, sai su dauki katin wurin aiki da kuma takardar biza ta izinin shiga Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel