Adams Oshiomhole ne ya koya mun yadda ake fada da ubangida – Gwamna Obaseki

Adams Oshiomhole ne ya koya mun yadda ake fada da ubangida – Gwamna Obaseki

- Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo yace ya koyi yadda ake fada da ubannin gidan siyasa ne daga tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomhole

- Obaseki ya bayyana cewa zai koyar da manufofin fada da ubannin gida idan har hakan zai amfani mutanen Edo saboda kudin da ke zuwa ga ubannin gidan a yanzu ya koma ga mutanen

- Gwamnan yayi zargin cewa rikicin da ya kunno kai a majalisar dokokin jihar aikin wani ne da ke son amfani da yan majalisar wajen juya shi

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomhole ne ya koya mishi yadda ake fada da ubannin gida a harkar siyasa.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Obaseki yayi jawabin ne lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin wakilai na majalisar dokokin jihar domin duba lamarin rikicin majalisar dokokin Edo.

Da yake magana ta hannun Philip Shaibu, mataimakinsa, gwamnan ya bayyana cewa Oshiomhole wanda a yanzu shine Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa ne ya fara jihadin yakar ubannin gida na siyasa a Edo a 2006.

Ya kuma jadadda cewa zai koyar da manufofin fada da ubannin gida idan har hakan zai amfani mutanen Edo saboda kudin da ke zuwa ga ubannin gidan a yanzu ya koma ga mutanen.

KU KARANTA KUMA: An kama wani malamin makaranta dumu-dumu yana lalata da dalibansa yara mata uku

Gwamnan yayi zargin cewa rikicin da ya kunno kai a majalisar dokokin jihar aikin wani ne da ke son amfani da yan majalisar wajen juya shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel