Matawalle ya ajiye mutane fiye da 100 da aka ceto daga wajen yan ta’adda a gidan gwamnati

Matawalle ya ajiye mutane fiye da 100 da aka ceto daga wajen yan ta’adda a gidan gwamnati

-Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ta ajiye mutane 109 da aka ceto daga hannun yan ta’adda a gidan gwamnati dake a Gusau

-Gwamna Bello Matawalle ya kirkiri shirin yin sulhu da yan ta’adda a sati uku da suka wuce inda ya kafa kwamitin yin sulhun wanda komishinan yan sanda na jihar Usman Nagoggo ke jagoranta

-Gwamna Matawalle ya bayar da umurnin a sama ma mutanen wajen zama da abinci sa’annan kuma a duba lafiyarsu

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ta ajiye mutane 109 da aka ceto daga hannun yan ta’adda a gidan gwamnati dake a Gusau.

A jawabin da babban daraktan hulda da jama’a na gwamnan jihar Alhaji yusuf idris, ya fitar, ya bayyana cewa an ceto mutanen da suka hada da maza da mata da yara daga hannun yan ta’adda ta hanyar sulhu da gwamnan jihar ya kirkira.

Gwamna Bello Matawalle ya kirkiri shirin yin sulhu da yan ta’adda a sati uku da suka wuce inda ya kafa kwamitin yin sulhun wanda komishinan yan sanda na jihar Usman Nagoggo ke jagoranta.

An baiwa kwamitin alhakin ganawa da yan ta’addan da shugawabanninsu don a samu a ceto mutanen da suka yi garkuwa da su.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa kasa da kwanaki 10 da kaddamar da shirin sulhun, an samu nasarar ceto mutane 109 daga hannun yan ta’adda daban daban.

A ranar Alhamis 11 ga watan Yuli 2019, sarkin Zurmi, Alhaji Abubakar Atiku ya mika mutane 14 da aka ceto ga gwamnatin jihar, inda gwamna Matawalle ya bayar da umurnin a sama ma mutanen wajen zama da abinci sa’annan kuma a duba lafiyarsu.

KARANTA WANNAN: Tirkashi: Amaechi ya fede biri har wutsiya, ya bayyana 'yan siyasar da suka sace kudi suka azurta kansu a kasar nan

Ya bayyana cewa "Na san cewa yan uwanku sun kagara su ganku kun dawo gida, amma tsayawarku nan na da mahimmanci don tabbatar da cewa kun samu kulawa ta musamma akan lafiyarku, ta yadda lokacin da za ku koma gida, za ku isa a cikin koshin lafiya.”

Gwamnan ya yaba ma komishinan yan sanda na jihar Usman Nagoggo da yan kwamitinshi akan irin aiki mai kyau da suke yi, sa’annan kuma yayi alkawarin ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro har sai an magance duk matsalolin tsaro a jihar.

Komishinan yan sanda ya bayyana ma gwamnan cewa wasu daga cikin wadanda aka ceto yan makwabtan jihohin Katsina, Kano, Sokoto, Kebbi da Kaduna ne, wasun su kuma yan kasar Nijar ne. (NAN)

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel