Kudirin tare makamai a Najeriya ya jawo sabani tsakanin ‘Yan Majalisar Wakilai

Kudirin tare makamai a Najeriya ya jawo sabani tsakanin ‘Yan Majalisar Wakilai

Wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya sun nuna mabanbantan ra’ayi a tsakaninsu a wani zama da a ka yi Ramar Alhamis 11 ga Watan Yuni, 2019 a dalilin wani sabon kudiri da a ka gabatar.

Daily Trust ta rahoto cewa ‘dan majalisar APC, Hon. Tahir Monguno ya kawo wani kudiri da ke kokarin maganin barkowar makamai cikin Najeriya, wanda wannan ya jawo takkadama a zauren.

Yanzu dai wannan kudiri ya samu karbuwa zuwa mataki na biyu a majalisar kasar, duk da cewa da fari an samu wasu ‘yan majalisa da su ka nuna rashin bada goyon baya ga wannan kudiri.

Daga cikin abubuwan da wasu ‘yan majalisa ba su gamsu da shi ba a kan wannan kudiri shi ne kokarin cirewa ‘yan sanda karfi wajen datse makamai tare da daura nauyin kan wata hukuma.

KU KARANTA: Cacar baki ya kaure tsakanin Masoya Atiku Abubakar da Shugaba Buhari

Idan wannan kudiri ya samu shiga, za a kafa wata hukuma ta musamman da za ta rika duba halin shiga da ficen manya da kananan makamai daga kasashen ketare zuwa cikin gida Najeriya.

Daga cikin wadanda su ka nuna rashin goyon baya kada’an ga wannan kudiri na Tahir Munguno, akwai Honarabul Umar Bago, wanda ya ke ganin a bar wa ‘yan sandan Najeriya wannan aiki.

Shi ma wani ‘Dan majalisar APC daga Kano, Hon. Aminu Sulaiman, ya goyi bayan Umar Bago. ‘Dan majalisar ya ce a na sa ra’ayin ya fi dacewa a maida hankali a kan hakkokin ‘yan sanda.

Wasu ‘yan majalisa irin su Hon. Yusuf Gagdi da Abdulrazak Namdas sun yi murnar jin labarin shigowar wannan kudiri wanda su ke ganin zai inganta tsaro, ganin irin gazawar ‘yan sanda.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel