Buhari ya bayar da umurnin kamo wadanda suka kashe diyar shugaban Afenifere

Buhari ya bayar da umurnin kamo wadanda suka kashe diyar shugaban Afenifere

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan Cif Reuben Fasoranti kan rasuwar diyars mai shekaru 58, Mrs Funke Olakunrin.

Kamar yadda mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya sanar, Shugaban kasar ya umurci hukumomin tsaro su bazama domin kamo miyagun da suka aikata wannan mummunan aikin cikin gaggawa.

Rahotanni sun ce 'yan bindigan sun harbe marigayiyan ne a ranar Juma'a a kan hanyar Kajola-Ore a jihar Ondo.

DUBA WANNAN: Za a biya tsohon gwamnan PDP da ke gidan yari N151.1 a matsayin kudin fansho

'Yan sanda sun yi hasashen cewa 'yan fashi da makami ne.

Shugaban kasar ya yi addu'a Allah ya bawa Pa Fasoranti juriya da hakurin babban rashin da ya yi.

A baya, Legit.ng ta rahoto cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar shima ya yi tir da kisan gillar da aka yi wa Misis Funlke Olakunrin.

A sakonin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya ce mace macen ya yi yawa.

Ya ce, "Ina Allah wadai da kisar Mrs Funke Olakunrin diyar shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere Chief Reuben Fasoranti. Wannan kashe-kashen ya yi yawa."

"Ina jira da hukumomin tsaro su fara binciken gaggawa domin gano wadanda suka aikata wannan mummunan aikin a kasar mu. Ina mika ta'aziyya ta ga Cif Reuben Fasoranti, iyalansa da dukkan mambobin Afenifere.

"Ni da iyalai na muna tare da ku a wannan lokacin bakin cikin a yayin da muke addu'ar Allah ya jikan Mrs Funke Olakunrin. Za a samu zaman lafiya a Najeriya ta kowanne hanya. Wannan abin ya isa haka!"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel