Duk mai neman aiki a Kaduna ya samu Mataimakiyata - Inji Gwamna El-Rufai

Duk mai neman aiki a Kaduna ya samu Mataimakiyata - Inji Gwamna El-Rufai

A cikin makon nan da ya gabata ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya nada sababbin Kwamishinonin da majalisa ta tantance. Daga ciki an yi watsi da mutun 1 da a ka zaba.

Gwamnan ya rantsar da wadannan Kwamishinoni na sa inda ya bayyana masu ayyukan da ke gabansu. Nasir El-Rufai ya kuma yi kira ga masu sha’awar aiki da gwamnatinsa, su aiko sunayensu.

Malam El-Rufai ya bayyana cewa duk wanda ya ke da burin aiki da gwamnatin jihar Kaduna a kan kowane mukami ne, zai iya aika sunansa da takardunsa zuwa ofishin mataimakiyar gwamnan jihar.

Gwaman ya nuna cewa Mataimakiyar ta sa watau Hadiza Balarabe, ita ce ke kula duk abin da ya shafi daukar aiki a jihar Kaduna; inda ta ke duba takardun jama’a ta nemi ma’aikatar da ta fi dacewa da su.

KU KARANTA: Za mu yi waje da duk Kwamishinan da ba ya aiki - El-Rufai

Kamar yadda labari ya zo mana a jiya Juma’a, 12 ga Watan Yuni, 2019, gwamnan ya bayyana cewa kwanan nan ya ruguza majalisar da ke kula da ma’aikatu da hukumomin jihar domin yin sababbin-zubi.

Sai dai duk da haka, gwamnan ya nuna cewa ba zai manta da ‘yan kishin kasa da Masoya jihar Kaduna ba da kuma dinbin jama’an da su ka taimaka da gumin su wajen samun nasarar APC a 2019 ba.

A cewar gwamna Nasir El-Rufai, ba za su yi kasa a gwiwa ga wadanda su ka yi duk wani fadi-tashi a lokacin zabe domin ganin jam’iyyarsu ta APC mai mulki ta samu gagarumar nasara ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel