An ci Facebook tarar dala biliyan biyar ($5bn)

An ci Facebook tarar dala biliyan biyar ($5bn)

-An kakabawa Facebook tarar dala biliyan biyar

-Hukumar cinikayya ta Amurka ce ta sanya wannan tarar ga kamfanin Facebook inda a yanzu ake jiran amincewar ma'aikatar shari'a domin kai karshen maganar

-Mamallakin kamfanin na Facebook Mista Mark Zuckerberg har yanzu bai ce komi ba kan wannan tara da aka daura ma kamfaninsa

Hukumar cinikayya ta Amurka ta ci tarar kamfanin sadarwa na Facebook dala biliyan biyar a matsayin diyya ga binciken da aka gudanar kan bayanan sirrin masu amfani da shi.

Wasu ‘yan adawa sun dade suna magana a kan a dauki mataki mai tsauri kan Facebook da kuma shugabansa Mark Zuckerberg.

KU KARANTA:Zan sauke duk kwamishinan da ya gagara yin aikinsa – El-Rufa’i

Wannan tarar zata iya zama tara mafi girma da hukumar ta sanyawa wani kamfanin fasaha, a halin yanzu dai ma’aikatar shari’a ake jira ta amince da hakan kafin a kai karshen batun.

Ko da yake dai babu wani cikakken bayanin da aka fitar a kan lamarin, amma wasu na ganin cewa matakan da za’a dauka kan Facebook din zasu kasance masu tsauri.

Haka zalika wasu mutanen na da ra’ayin cewa shi kan shi mamallakin kamfanin Mista Zuckerberg ya kamata a hukunta shi.

Shugabar cibiyar Dimokuradiyya da Fasaha, Nuala O’Connor ta ce tarar na nuna muhimmancin da bayanan sirrin ke da shi ga masu amfani da shafin.

Ta cigaba da cewa, an jima ana gargadin kamfanoni su yi kokarin kare bayanan sirrin da suka shafe su kuma wannan ya hada har da Facebook.

Har zuwa yanzu dai babban shafin sada zumuntar bai maida martani ba kan wannan batun ba. Kididdiga ta nuna a rubu’in farko na wannan shekarar mutum biliyan biyu da miliyan 38 ne su kayi amfani da shafin babu kakkautawa a ko wane wata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel