Ta tabbata: INEC da jam'iyyar APC sun yi aringizon sama da rumfuna 1,000 a jihar Borno - Jami'in jam'iyyar PDP

Ta tabbata: INEC da jam'iyyar APC sun yi aringizon sama da rumfuna 1,000 a jihar Borno - Jami'in jam'iyyar PDP

- Wani jami'in babbar jam'iyyar adawa ta PDP ya bayyana cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta kara sama da rumfuna 1,000 a jihar Borno

- Ya bayyana cewa hukumar zaben ta hada baki da jam'iyyar APC mai mulki ta yi wannan cuwa-cuwa a jihar ta Borno

- Ya kara da cewa a iya sanin shi rumfunan zabe 3,933 a jihar Borno, amma kawai sai yaga lokaci daya sun karu sun zama 5,078

Wani jami'in jam'iyyar PDP wanda yayi aiki a lokacin zaben shugaban kasa na 2019, ya bayyanawa kotun sauraron kararrakin zabe cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta kara rumfunan zabe sam da 1,000 a jihar Borno.

Mutumin ya kara da cewa hukumar zaben ta hada baki da jam'iyyar APC mai mulki ta yi wannan cuwa-cuwa a lokacin da ake gabatar da zaben shugaban kasa na watan Fabrairun wannan shekarar.

Jami'in mai suna Nicolas Shediza, shine babban jami'in jam'iyyar PDP mai kula da tattara sakamakon zabe na jihar Borno.

KU KARANTA: San barka: Mace ta farko a Arewa da ta fara kaiwa mukamin Manjo a hukumar soji

Ya bayyanawa kotun sauraron kararrakin zabe dake Abuja, ranar Alhamis din nan data gabata cewa jihar Borno na da rumfuna 3,933 na zabe, amma kuma kawai sai ya ga lokaci daya rumfunan nan sun karu sun zama 5,078.

Shediza ya kara da cewa a iya sanin shi, mutane 919,786 aka tabbatar da cewa sun jefa kuri'a a jihar Borno, amma kuma wadanda hukumar zabe ta bayyana sun wuce wannan yawan.

Sai dai kuma Shediza bai bayyana adadin yawan mutanen da ya ce hukumar zaben ta tantance ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel