Shaidun ADC sun bayyana ma kotun zabe cewa cin hanci aka basu don su fadi karya

Shaidun ADC sun bayyana ma kotun zabe cewa cin hanci aka basu don su fadi karya

-An sha mamaki a kotun zaben gwamna ta jihar Rivers bayan da shaidun dan takarar gwamna na jam’iyyar ADC suka bayyana cewa cin hanci aka basu don su ba da shaidar karya

-Shaidun guda biyu sun bayyana gaskiya a lokacin da lauyan gwamnan jihar Rivers, Emmanuel Ukala (SAN) yake tantance gaskiyar shaidar da suka bada

A jiya Juma’a ne aka sha mamaki a zaman sauraron kara a kotun zaben gwamna ta jihar Rivers bayan da shaidun dan takarar gwamna na jam’iyyar ADC, Victor Fingesi, suka bayyana ma kotu cewa cin hanci aka basu don su ba da shaidar karya.

Shaidun guda biyu sun bayyana gaskiya a lokacin da lauyan gwamnan jihar Rivers, Emmanuel Ukala (SAN) yake tantance gaskiyar shaidar da suka bada.

Shaida na 19 sha tara na jam’iyyar ADC, mai suna, Igoniko Gbabinyaa, ya bayyana cewa gaskiya bashi bane mai tattara sakamako na jam’iyyar ADC a karamar hukumar Ahoade, saboda sunan da aka yi anfani da shi akan takardar rubutacciyar shaida, Stanley Okereke, ba sunanshi bane.

Ya bayyana cewa dan takarar jam’iyyar ADC da ya sha kaye a zaben gwamna da ya gabata ne ya dauko shi dan ya bada shaidar karya.

Haka zalika, shaida na 20 na jam’iyyar ADC da ya bayyana sunanshi a matsayin Madume Okei, ya ce imaninshi ya motsa shi ya sanya ya ga ya kamata ya fadi gaskiya duk da cewa ya karbi cin hanci daga wajen dan takarar ADC.

KARANTA WANNAN: Jarumar fina finan hausa, Nafisa Abdullahi za ta zama daraktar fina finai

Ya bayyana ma kotun cewa shi ba ma dan jam’iyyar ADC bane kuma bai ta ba yi ma jam’iyyar aikin tattara sakamakon zabe a Ahoada ba.

Okei ya bayyana ma kotun cewa bashi bane ya rubuta rubutacciyar shaida da dan takarar jam’iyyar ADC ya gabatar.

Ya bayyana cewa ya samu kira daga wajen abokansa ana sauran kwanaki kadan a fara sauraron kara, inda suka bukace shi da ya bayar da shaida ga Fingesi. Ya bayyana cewa sauran abokan nashi ma na cikin shirin bada shaidar karyar.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel