Wani abu sai Najeriya: Kwantena biyu da gwamnatin tarayya ta sayo na kayan gyaran wutar lantarkin sun yi batan dabo a tashar jiragen ruwa

Wani abu sai Najeriya: Kwantena biyu da gwamnatin tarayya ta sayo na kayan gyaran wutar lantarkin sun yi batan dabo a tashar jiragen ruwa

- An sace wasu kwantenoni guda biyu da gwamnatin tarayya ta sayo kayan gyaran wutar lantarki daga turai

- Kwantenonin guda uku wanda aka ciko su da kayan, biyu daga ciki sunyi batan dabo, yayin da dayar da ta rage ita ma aka gane cewa babu komai a cikinta

- Sai dai babban daraktan hukumar TCN din bai bayyana ainahin tashar jiragen ruwan da kwantenonin suka bace ba

Cibiyar kula da wutar lantarki ta Najeriya (TCN) ta bada tabbacin wani al'amari da ya faru mai kama da almara, cibiyar ta sanar da yadda wasu manyan kwantenoni da gwamnatin tarayyar Najeriya ta sayo daga kasashen waje, wadanda suke cike da kayan da za ayi gyaran wutar lantarkin kasar nan suka bace babu amo babu labari.

Abin da ya bada mamaki shine yadda aka bayyana cewa kwantenoni biyu daga cikin guda uku da gwamnati ta sayo sun yi batan dabo a wata tashar jiragen ruwa na kasar nan.

KU KARANTA: San barka: Mace ta farko a Arewa da ta fara kaiwa mukamin Manjo a hukumar soji

Sannan ita ma dayar kwantenar da ta rage da aka bude ta an tarar da babu komai a cikinta, inda ake zargin cewa wasu ne suka wawushe kayan cikin.

Babban Daraktan cibiyar kula da wutar lantarkin na Najeriya (TCN), Usman Gur Mohammed, shine ya bayyana hakan ranar Larabar nan da ta gabata a babban birnin tarayya Abuja, amma kuma daraktan bai bayyana ainahin tashar jiragen ruwan da kwantenonin suka bace ba.

An shafe shekara da shekaru dai ana fama da matsalar wutar lantarki, wacce har yanzu taki ci taki cinyewa.

A lokuta da dama akan samu tallafi daga kasashen ketare ko kuma gwamnati tayi kokarin gyarawa da kanta, amma hakan baya yiwuwa saboda wasu tsirarun mutane da za su kawowa matsala domin ganin wannan aiki bai yiwuwa ba

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel