Wata budurwa ta guntulewa saurayinta Azzakari da hakori, an damketa

Wata budurwa ta guntulewa saurayinta Azzakari da hakori, an damketa

Hukumar yan sandan jihar Legas ta damke wata budurwa yar shekara 20 da haihuwa, Blessing John, kan laifin guntulewa saurayinta, Johnson, azzakari yayinda yake kokarin yi mata fyade. A cewarta.

Blessing wacce ke tsare a sashen binciken hukumar dake Panti, Yaba Legas ta bayyanawa manema labarai cewa ta aikata wannan abu saboda halin da ta samu kanta na azaba a lokacin.

Tace: "Johnson saurayina na; yana aika a Otal. Mun fara soyayya watanni shida da suka gabata kuma ya yi mini alkawarin shirya min takardan neman aiki, sai ya bukaci in sameshi a gidan abokinsa dake Surulere a ranar 5 ga watan Yuli."

"Da na isa gidan abokinsa, sai muka je mashaya inda shi da abokinsa suka kwankwadi giya. Sai suka bukaci in bisu gidan wani dan'uwansu amma na ki, nace ina son wucewa gida da wuri."

Sai muka koma gida, sai na tambayesa ina takardar, sai yace bai kawo ba kuma gashi nace ina son wucewa."

KU KARANTA: Zan sauke duk kwamishinan da ya gagara yin aikinsa – El-Rufa’i

"Sai yayi fushi, yana mai cewa ta yaya zan zo kuma kawai in tafi haka. Sai na fada masa menene amfanin tsayawa tunda ba zam samu abinda ya kawoni ba."

"Sai yayi kokarin cire min kaya kuma ya waska min mari sau biyu saboda na ki. Sai ya cire kayansa, ya danne a kasa."

"Johnson ya lashi takobin cewa sai yayi lalata dani, amma da na ki sai ya dokeni a baya, zafin haka ya sa na cije masa azzakari. Ban yi nufin cutar da shi ba."

Blessing tace da wuri aka garzaya da shi asibiti a Surulere inda likitoci suka ki dubashi har sai wani dan uwansa ya halarto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel