Zan sauke duk kwamishinan da ya gagara yin aikinsa – El-Rufa’i

Zan sauke duk kwamishinan da ya gagara yin aikinsa – El-Rufa’i

-El-Rufai ya gargadi sabbin kwamishinoninsa kan cewa kada su sake suyi wasa da aikinsu

-Gwamnan ya yi wannan gargadin a yayin da yake rantsar da kwamishinonin su 13 bayan da majalisar dokokin jihar Kaduna ta aminta da nadinsu

-Daya daga cikin sunayen da gwamnan ya tura majalisar ta qi amincewa da nadinsa saboda ya taba sukar gwamnatin El-Rufai a shafinsa na Facebook

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya ci alwashin cewa zai sauke duk kwamishinan da ya kasa yin abinda aka daura shi a kai.

Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a ranar Juma’a lokacin da yake rantsar da sabbin kwamishinoni 13 wadanda suka samu yarjewar majalisar dokokin jihar Kaduna.

KU KARANTA:Duniya ina zaki damu: Wata mata ta kashe ubangidanta kan ya qi biyanta N525

Ya kara da cewa; daga lokaci zuwa lokaci zai rika bibiyar ayyukan kwamishinonin, a don haka ya ba wa sabbin kwamishinonin shawarar su yi shirin fara aikinan take.

Ga abinda El-Rufai ya fadi cikin kalamansa: “ Ya zama wajibi a gareku ku shirya yin aiki. Ko wane daya daga cikin ku zai samu bayani a kan yadda aikin nasa yake sannan kuma zamu rika bibiyar yadda aikin naku ke tafiya.

“ Akwai buqatar ko wane dayanku ya sanya hannu kan tsarin KPI wanda zai rika auna jajircewarsa da kuma kokarinsa kan aikin da aka sa shi. Daga lokaci zuwa lokaci zamu rika bincikar ayyukanku, saboda farantawa jama’armu shi ne burinmu.”

Gwamnan ya sake yin kira ga iyalan kwamishinonin da su bai wa ahalin nasu goyon bayan da suke buqata a daidai lokacin da suka kama aiki.

Har ila yau, Gwamna El-Rufai ya bai wa mataimakiyarsa, Hadiza Balarabe damar rike ma’aikatar lafiya ta jihar gabanin a nada mata na ta kwamishinan na musamman.

Haka zalika, majalisar dokokin jihar ta qi amincewa da Jaafaru Abubakar a matsayin kwamishina saboda ya taba sukar gwamnatin El-Rufai a kafar sada zumunta ta Facebook.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel