Yanzu-yanzu: Atiku ya yi tir da kisar gillar da aka yi wa diyar Farosanti

Yanzu-yanzu: Atiku ya yi tir da kisar gillar da aka yi wa diyar Farosanti

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi allah wadai da kisar Misis Funke Olakunrin, diyar shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere Chief Reuben Fasoranti da wasu 'yan bindiga suka kashe.

An harbe Olakunrin ne a ranar Juma'a a Ore, hedkwatan karamar hukumar Odigbo na jihar Ondo.

A sakonin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya ce mace macen ya yi yawa.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Mutum 5 da suka mallaki arzikin da ya fi kasafin kudin Najeriya

Ya ce, "Ina Allah wadai da kisar Mrs Funke Olakunrin diyar shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere Chief Reuben Fasoranti. Wannan kashe-kashen ya yi yawa."

"Ina jira da hukumomin tsaro su fara binciken gaggawa domin gano wadanda suka aikata wannan mummunan aikin a kasar mu. Ina mika ta'aziyya ta ga Cif Reuben Fasoranti, iyalansa da dukkan mambobin Afenifere.

"Ni da iyalai na muna tare da ku a wannan lokacin bakin cikin a yayin da muke addu'ar Allah ya jikan Mrs Funke Olakunrin. Za a samu zaman lafiya a Najeriya ta kowanne hanya. Wannan abin ya isa haka!"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel