Assha: An maka limamin coci a gaban kuliya kan damfarar N980,000

Assha: An maka limamin coci a gaban kuliya kan damfarar N980,000

An gurfanar da wani limanin coci mai shekaru 52, Adebola Olufowobi a gaban kotun majistare da ke Agbowa bisa zarginsa da damfarar wata 'yar cocinsa zunzurutun kudi N980,000.

'Yan sanda sun zargi Olufowobi da aikata laifuka guda uku masu alaka da damfara da barzanar ga rayuwa.

Sai dai bai amsa tuhumar da ake masa ba.

Dan sanda mai shigar da kara, Saja Yomi Egunjobi ya shaidawa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne tsakanin Nuwamban 2010 zuwa Nuwamban 2012 a unguwar Igbobgbo da ke Ikorodu a Legas.

DUBA WANNAN: Jonathan ya roki wata alfarma ta musamman a wurin gwamnatin Buhari

Ya ce wanda ake zargin ya damfari wata yar cocinsa, Shakirat Ajagbe inda ya karbe mata N980,000 du sunnan za a sayar mata da fili har da ginanen daki guda a filin.

Ya kuma bukaci kudi a hannun ta na sayan bulo da yashi da duwatsu kuma duk ta bashi har ma da kudin rufi N100,000.

Ya ce a lokacin da Ajabge ta nemi a kai ta ta ga gidan ta sai ya fara mata kame-kame.

Laifin ya sabawa sashi na 287, 314 da 230 na Criminal Law na jihar Legas na shekarar 2015.

Alkalin kotun, A.O Ogbe ta bayar da belin wanda ake tuhumar kan kudi N500,000 tare da ganbatar da mutane biyu da za su karbi belinsa.

Ya daga cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 28 ga watan Augusta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel