Buhari ya yi wa Ja'afaru Ahmed karin wa'adi a matsayin shugaban NPS

Buhari ya yi wa Ja'afaru Ahmed karin wa'adi a matsayin shugaban NPS

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Ja'afaru Ahmed karin wa'adin shekara daya a matsayin Kwantrola Janar na Hukumar Kula da Gidajen Yari

- Shugaban kasan ya yi masa karin wa'adin ne saboda sauye-sauye masu amfani da ya kirkiro a hukumar da akwai bukatar ya karasa

- Shugaban kasar ya bukaci Mista Ja'afaru ya cigaba da jajircewa kan aikinsa da yi wa kasa hidima

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da yi wa shugaban Hukumar Kula Da Gidajen Yari na Kasa (NPS), Ja'afaru Ahmed karin wa'adi na shekara guda da za ta fara daga ranar 21 ga watan Yuli.

Sanarwar da ta fito daga mai magana da yawun hukumar harkokin cikin gida, Mohammed Manga ya ce an yi wa Ja'afaru karin wa'adi na shekara guda daya ne saboda "irin ayyukan masu kyau da ya faro a hukumar kula da gidajen yarin da duka hada da kulawa da hakkin dan adam, inganta kiwon lafiya, ilimi na ayyukan noma na fursunoni da akwai bukatar ya kammala."

DUBA WANNAN: Jonathan ya roki wata alfarma ta musamman a wurin gwamnatin Buhari

Bayan taya shi murna kan karin wa'adin da akayi masa, Famanen Sakataren Hukumar Harkokin Cikin Gida, Georgina Ehuriah ya bukaci shi ya cigaba da sauye-sauyen da ya faro na yin garambawul kan tsarin kulawa da fursunonin kan tsarin gwamnati mai ci a yanzu.

Kafin nadinsa a matsayin Kwantrola Janar, Mista Ja'afaru ya shugabanci gidajen fursuna da dama a kasar.

Ya kuma rike mukamin mataimakin Kwantrola Janar a sashin mulki da samar da kayayaki a Hedkwatan Hukumar da ke Birnin Tarayya, Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel