Hukumar Kwastam na asarar akalla jami'ai 2000 a kowani shekara

Hukumar Kwastam na asarar akalla jami'ai 2000 a kowani shekara

Hukumar hana fasa kwabri, Kwastam, ta ce ana asarar jami'an hukumar akalla 2000 a kowani shekara wajen yaki da masu kokarin shigo da kayayyaki ta barauniyar hanya cikin Najeriya.

Kwantrola Janar na hukumar, Kanar Hameed Ali, ya bayyana hakan ne a ganawar da babbar bankin Najeriya CBN ta shirya tare da manyan hafsoshin hukumomin tsaron Najeriya.

Sauran da suka halarci ganawar sune masu ruwa da tsaki a ma'aikatun auduga da masaka.

Hameed Ali, wanda ACG Abdullahi Babani, ya wakilta ya bayyana cewa fasa kwabri na daya daga cikin manyan kalubale da hukumar ke fuskanta kuma ya zama wajibi a yakeshi.

Kwantrola Janar ya nuna damuwarsa kan yadda fasa kwabri ya yawaita a fadin kasar nan kuma hukumar na iyakan kokarinta wajen ragewa.

KU KARANTA: An gurfanar da yan Shi'a 38 a gaban kotu

Abdullahi Ali ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta inganta ka'idojin kudi domin taimakawa wajen hana fasa kwabri musamman na kayayyakin sawa.

Yace:"Akwai bukatar gwamnati ta gyara ka'idojin kudi; gina hanyoyin mota, inganta tsaro, gyara wutar lantarki, domin ma'aikatun cikin gida su iya gudanar da aiki."

"Idan aka samar da wadannan, abubuwan da ake kerawa a Najeriya zasuyi sauki kuma mutane zasu daina damuwa da wadanda ake shigo dasu daga kasashen waje; wanda shine yasa fasa kwabri ke bunkasa."

Hakazalika, shugaban Kwastam ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a ma'aikatun saka su taimaka wajen baiwa jami'an tsaro labarin masu fasa kwabri domin taka musu birki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel