Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe diyar shugaban Afenifere

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe diyar shugaban Afenifere

Wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya fulani ne sun kashe Misis Funke Olakunrin diyar shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere, Cif Ruben Fasoranti.

Funke Olakunrin ta mutu tana da shekaru 58 a duniya.

A cewar wadanda abin ya faru idanunsu, Olakunrin da mutu ne sakamakon raunin bindiga da wasu da ake zargin makiyaya ne suke harbe ta a Ore Junction da ke jihar Ondo a ranar Juma'a.

DUBA WANNAN: Jonathan ya roki wata alfarma ta musamman a wurin gwamnatin Buhari

Punch ta ruwaito cewa mai magana da yawun kungiyar, Yinka Odumakin yana cewa kungiyar ta samu rahoton cewa makiyay ne suka kashe diyar shugaban kasa.

A cewar Odumakin, matar mai shekaru 58 ta baro Akure kan hanyar ta na zuwa Ore junction 'yan bindigan suka kai mata hari.

"Mun tabbatar da rasuwar Misis Funke Olakunrin, diyar shugban mu, Cif Fasoranti," inji shi.

"Ta baro Akure ne lokacin da makiyayan suka fito daga daji suke tare motar ta da wasu motoccin.

"Mai taya ta hidima da ke cikin motar itama ta samu raunin bindiga. Mun gaji da wannan kashe-kashen."

Hakan na zuwa ne lokacin da ake yawan fama da yawan fashi da makami da garkuwa da mutane a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel