Babbar magana: Buhari ya sanya al'umma cikin talauci da bala'in yunwa fiye da yadda suke a 2015 - Atiku

Babbar magana: Buhari ya sanya al'umma cikin talauci da bala'in yunwa fiye da yadda suke a 2015 - Atiku

Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayya cewa dukkanin yan Najeriya a yanzu na fama da talauci fiye da yadda suke a 2015 sau biyu.

Atiku ya bayyana hakan ne a shafinsa na twitter a ranar Juma’a, 12 ga watan Yuli.

Ya rubuta a shafinsa: “A yadda yake a yau, duk wani mutum, namiji, mace, da yara a Najeriya a yanzu yana fama da talauci fiye da yadda yake a 2019, bugu da kari, dukkaninmu mun talauce sau biyun yadda muka yi a 2015. ba lallai ne mun taimaka wajen yin yawan rance ba, amma dukkaninmu muna shan radadin lamarin.”

A wani lamari na daban, kotun daukaka kara dake zaune a Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar kan shugaba Muhammadu Buhari na bukatar hanashi takara kujeran shugaban kasa saboda kwalayen karatunsa.

KU KARANTA KUMA: Kai jama’a: Wata mata ta kona mijinta saboda zai mata kishiya a jihar Kano

Shari'ar da kotun tayi a ranar Juma'a ta ce an shigar da wannan karar bayan lokacin shigar da kara kan abubuwan da suka faru kafin zabe ya shude.

Wadanda suka shigar da karar, Kalu Kalu, Labaran Ismail da Hassy Kyari el-Kuris, sun garzaya kotun daukaka kara ne bayan babban kotun tarayya tayi watsi da karar tun farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel