Duniya ina zaki damu: Wata mata ta kashe ubangidanta kan ya qi biyanta N525

Duniya ina zaki damu: Wata mata ta kashe ubangidanta kan ya qi biyanta N525

-Wata matashiya ta dabawa ubangidanta wuka bayan sunyi sa'insa a kan wasu 'yan kudi kalilan

-Matar ta kashe ubangidan nata ne a dalilin ya hanata N525 wanda yake kudin aikinta ne na ko wane yini

-Bayan tafka wannan ta'asa matar ta gudu saboda har a lokaci kawo maku wannan labarin babu wanda yasan wurin da take amma dai jami'an yan sanda na cigaba da nemanta

Wata mata mai suna Jesca Chesang mai shekaru 22, yar asalin kasar Kenya ta dabawa ubangidanta Joseph Kimutai Sang wuka inda ya mace har lahira a kan N525 kudin aikinta na ko wace rana.

Mun samu labari daga jaridar Punch cewa, fada ya kaure ne a tsakanin Chesang da ubangidanta Sang a lokacin da ta tunkare shi domin neman ya biyata haqqinta na yini daya, Ksh 150 wanda yayi daidai da N525 a kudin Najeriya.

KU KARANTA:Zaben 2019: Yau Atiku zai gabatar da bidiyo matsayin shaida a kotu

A daidai lokacin da ya qi ya biyanta wannan kudi sai hayaniya ta kaure a tsakininsu daga nan ta daba masa wuka a baya ta gudu.

An yi gaggawar kai Sang asibiti domin ceto rayuwarsa sai dai kash, ko da aka isa asbitin ya riga da ya ce ga garinku nan.

Rahotanni daga Citizen TV, sun bayyana mana cewa hukumar ‘yan sandan Kericho sun baza jami’ai domin neman wannan mata kana kuma an kai gawar dakin ajiyar gawarwaki na asibiti domin ajiya.

Ita dai wannan matashiyar kafin ta tafka wannan aika-aika ta kasance mai tsinko gayen shayi ne a gonar shi marigayin inda yake biyanta Ksh 150 daidai da N525 kenan a kudin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel