Yanzu-yanzu: Buhari ya samu nasara, kotu ta yi watsi da karar masu tuhumar kwalin karatunsa

Yanzu-yanzu: Buhari ya samu nasara, kotu ta yi watsi da karar masu tuhumar kwalin karatunsa

Kotun daukaka kara dake zaune a Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar kan shugaba Muhammadu Buhari na bukatar hanashi takara kujeran shugaban kasa saboda kwalayen karatunsa.

Shari'ar da kotun tayi a ranar Juma'a ta ce an shigar da wannan karar bayan lokacin shigar da kara kan abubuwan da suka faru kafin zabe ya shude.

Wadanda suka shigar da karar, Kalu Kalu, Labaran Ismail da Hassy Kyari el-Kuris, sun garzaya kotun daukaka kara ne bayan babban kotun tarayya tayi watsi da karar tun farko.

A shariar kotun daukaka karar, Alkali Mohammed Idris a madadin sauran Alkalan ya amince da shari'ar babban kotun tarayyan kuma ya sake watsi da karar.

KU KARANTA: An sake damke yan Shi'a 65 a Abuja

Mun kawo muku rahoton cewa Yau juma’a 12 ga watan Yuli 2019, kotun daukaka kara za ta yanke hukunci a tuhumar da ake yi ma shugaba Buhari akan can-cantarshi ta tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

A ranar 8 ga watan Yuli 2019, alkalai uku na kotun daukaka karar da Jastis Atinuke Akomolafe ke jagoranta sun sanaya ranar da za su yanke hukunci bayan da suka gama sauraron mahawara tsakanin lauyoyin masu shari’ar.

A zaman da akayi na karshe a kotun, lauyan masu daukaka kara, Ukpai Ukairo ya bayyana cewa shugaba Buhari bashi da cikakken ilimin da zai tsaya takarar kujerar shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel