Tashin hankali: Mu miliyan 21 ne, kuma a shirye muke mu bada rayuwarmu don ganin shugaban mu ya fito - 'Yan Shi'a

Tashin hankali: Mu miliyan 21 ne, kuma a shirye muke mu bada rayuwarmu don ganin shugaban mu ya fito - 'Yan Shi'a

- Kungiyar 'yan uwa Musulmai ta sha alwashin bayar da rayukan duka mabiyanta miliyan 21 don ganin shugaban su ya fito

- Sun ce a shirye suke suga sun mutu, mutukar ba a saki shugaban su ba wanda yake hannun gwamnatin tarayya a tsare

- Sun bayyana cewa tabbas yawansu ya kai miliyan 21 kuma sun san cewa yawan harsashin sojojin Najeriya bai kai wannan yawan ba

Kungiyar 'yan uwa Musulmai ta Najeriya wacce aka fi sani da Shi'a, ta gabatar da wata zanga-zanga a jihar Legas jiya Alhamis 11 ga watan Yuli.

'Yan kungiyar sun sha alwashin bayar da rayuwarsu gaba daya su miliyan 21 domin ganin shugabansu ya kubuta daga hannun gwamnatin tarayya.

Shugaban sun Malam Ibrahim El-Zakzaky ya na tsare a gurin gwamnatin tarayya tun watan Disambar shekarar 2015, bayan haduwar 'yan kungiyar da rundunar sojojin Najeriya a garin Zaria dake jihar Kaduna.

KU KARANTA: Birane guda 50 da suke da matukar hatsari a duniya ga matafiya

Shugaban kungiyar na yankin kudu maso yammacin Najeriya, Muftau Zakariya, wanda yayi magana da manema labarai a lokacin da suke gabatar da zanga-zangar, yayi kira ga jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu, da ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya saki shugaban nasu.

"A shirye muke mu mutu idan har basu saki shugaban mu ba. Idan har sun shirya kashe mu, muna da mabiya miliyan 21 da muke a shirye mu bada rayukan mu. Na san cewa sojojin Najeriya basu da harsashi miliyan 21 da zai kashe mu duka," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel