An kuma: Wasu mutum 163 sun dawo Najeriya daga Libya bayan sun galabaita

An kuma: Wasu mutum 163 sun dawo Najeriya daga Libya bayan sun galabaita

-Wadansu gungun 'yan Najeriya sun dawo gida daga kasar Libya a galabaice

-Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa ce ta bamu wannan labarin inda tace mutanen da suka dawon su 163 ne

-Daga cikin mutanen akwai yara kanana kai har ma jarirai maza da mata a cikinsu kamar yadda Ahaji Idris ya shaida mana

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa wato NEMA ta ce wata sabuwar tawagar mai dauke da ‘yan Najeriya 163 sun dawo gida daga kasar Libya.

Shugaban hukumar mai kula da sashen Kudu maso yammacin Najeriya, Alhaji Idris Muhammad ne ya karbi wadannan mutanen a madadin gwamnatin tarayya a filin sauka da tashin jiragen saman Kasa da Kasa na Murtala Muhammad dake Legas.

KU KARANTA:Zaben 2019: Yau Atiku zai gabatar da bidiyo matsayin shaida a kotu

Kungiyar kula da masu hijira ta kasa da kasa ce ta dawo da mutanen, a cikin jirgin saman Alburaq Air mai dauke da lamba kamar haka UZ 189/8738 da kuma 5A-DMG wanda ya iso Najeriya da misalin karfe 8:33 na daren Alhamis.

Daga cikin wadanda aka dawo da su din, 64 a cikinsu mata ne baligai, yara mata 4, jarirai mata 7, sai kuma maza baligai 75, yara maza 3 da kuma jarirai maza 10.

Alhaji Idris yayi kira na musamman ga matasa, na su bar sanya rayuwarsu cikin irin wannan hanyar da kan iya jefasu cikin mummunan hatsari.

Bugu da kari, ya sake cewa, aikin NEMA ne samar da agaji na musamman ga duk dan Najeriyar da ya jigata, a don haka hukumarsu ba zata yi qasa a gwiwa ba wajen bai wa wadannan mutanen irin taimakon da suke buqata ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel