Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shirin N-Power ya lashe N279bn

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shirin N-Power ya lashe N279bn

-Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa an kashe Naira biliyan 279 wajen biyan albashin yan aikin sa kai na N-power

-Shirin N-Power na daya daga cikin shirye shiryen da gwamnatin shugaba Buhari ta shigo da shi don tallafa wa mutane ta hanyar sama masu aikin yi da niyyar rage radadin talauci a kasar nan.

A yau Juma’a 12 ga watan Yuli 2019, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa an kashe Naira biliyan 279 wajen biyan albashin yan aikin sa kai na N-power tun sanda aka kaddamar da shirin a cikin watan Disamba na shekarar 2016.

Shirin N-Power na daya daga cikin shirye shiryen da gwamnatin shugaba Buhari ta shigo da shi don tallafa wa mutane ta hanyar sama masu aikin yi da niyyar rage radadin talauci a kasar nan.

Da yake zantawa da yan jarida, babban mai taimakawa shugaba Buhari kan samar da ayyukan yi ga matasa, Afolabi Imoukhuede ya bayyana cewa ana biyan Naira 30,000 ga mutane 500,000 dake aikin N-Power a kowanne wata.

Ya bayyana cewa babu mutum ko daya cikin masu yin aikin N-Power da ke bin gwamnatin tarayya bashin Kwabo daya.

A cewarshi, an kashe Naira biliyan 180 ga kashin farko na ma’aikata 200,000 da aka dauka a karkashin shirin na N-Power daga watan Disamba 2016 zuwa watan Yuni na shekarar 2019, inda ake biyan Naira biliyan 6 a kowanne wata.

KARANTA WANNAN: An yanke ma wani direba mai shekara 21 hukuncin shekaru 4 a gidan yari kan satar adaidaita sahu

An tambaye shi ko nawa aka kashe tun daga lokacin da aka kirkiri shirin, sai ya ce “Wannan abu ne mai sauki gane yawan kudaden da aka zuba ga mutane. Ina gaya maku cewa kashin farko sun fara karbar albashi tun cikin watan Disamba 2016, saboda haka an kashe kusan biliyan 72 a duk shekara ga kashin farko kawai. Wannan baya ga kudaden da aka kashe wajen sayen na’urori da kayayyakin aiki da aka basu horo."

Haka zalika ya bayyana cewa “Amma daga watan Agusta na shekarar da ta gabata, kudin sun tashi daga biliyan 6 zuwa biliyan 15 a kowanne wata saboda yanzu mutane 500,000 ne ake biya Naira 30,000 a kowanne wata."

Afolabi ya bayyana cewa an kirkiri shirin ne don magance matsalar rashin aikin yi da matsan Najeriya ke fama da shi

Ya bayyana cewa a yanzu haka ana shirin daukar wasu daga cikin yan N-Power din aikin dan sanda ta hanyar yin hadaka da gwamnonin jihohi don samar da tsaro a kauyuka.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel