Kotu ta bayar da belin uba mai shekara 60 da ya lalata yarsa mai shekara 8

Kotu ta bayar da belin uba mai shekara 60 da ya lalata yarsa mai shekara 8

Wani tsoho mai shekara 60, Mista Godwin Anukwa, wanda ake zargi da lalata yarsa mai shekara takwas, ya samu beli kan N500,000 a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli.

Wata kotun Majistare da ke zama a Ikeja, wacce ta ba wanda ake karar beli, ta bukace shi da ya kawo mutane biyu da za su tsaya masa a matsayin bangare daga cikin ka’idojin bayar da belin nasa.

Mai shari’a a kotun, Misis Yewande Aje-Afunwa, tayi umurnin cewa dole wadanda za su tsaya masa su kasance ma’aikata sannan su nuna hujjar biyan haraji ga gwamnatin jihar Lagas.

Aje-Afunwa ta kara da cewa ya zama dole daya daga cikin masu tsayawar su kasance da alaka da wanda ake karar.

Ana tuhumar wanda ake karar da laifin lalata.

sai dai kuma bai amsa laifinsa ba.

Da farko dai dan sanda mai kara, ASP Peter Nwangwu, ya fada ma kotu cewa wanda ake karar ya aikata laifin ne a watan Maris a yankin Isheri da ke Lagas.

KU KARANTA KUMA: An yanke ma wani direba mai shekara 21 hukuncin shekaru 4 a gidan yari kan satar adaidaita sahu

Nwangwu ya bayyana cewa wanda ake karar ya ci zarafin yar cikinsa ta hanyar tura mata yatsa a matancinta.

yace hakan ya saba ma okar jihar Lagas, kuma an tanadi hukuncin shekaru uku a gidan yari ga wanda ya aikata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel