Ku gafarce mu, makiyaya sun roki al’ummar Igbo

Ku gafarce mu, makiyaya sun roki al’ummar Igbo

-An yi zaman sulhu tsakanin al'ummar hausawa mazauna jihar Imo da kuma 'yan asalin jihar ta Imo

-Damian Zeru shi ne ya jagoranci ganawar kuma yace zai isar da duk abinda aka tattauna zuwa kunnen mai girma gwamna

-Shugaban hausawa mazauna Imo Suleman Ibrahim ya roki gafarar gwamnatin jihan kan laifin kisan da wasu makiyaya suka aikata a Obokofia

Wasu makiyayan da ake zargin sun kashe wani mazaunin Obokofia a karamar hukumar Ohaji/Egbema dake jihar Imo sun nemi gafara a kan abin da ya faru.

A wani zance da muka samu daga jaridar Vanguard, mun ji cewa, jiya a Owerri an yi zaman tattaunawa tsakanin Shugaban kwamitin sasantawa wato Damian Ezeru da kuma shugabannin kungiyar hausawa da makiyaya na yankin.

KU KARANTA:Zaben 2019: Yau Atiku zai gabatar da bidiyo matsayin shaida a kotu

Kamar yadda Ezeru ya fadi bayan an kammala ganawar, ya ce zai sanar da dukkan abinda aka tattauna zuwa ga Emeka Ihedioha, Gwamnan jihar Imo domin yanke hukunci na karshe a kan matsalar.

Har ila yau, rahotanni daga jaridar Vanguard sun shaida mana cewa daga cikin wadanda akayi ganawar da su akwai, jami’an tsaro na DSS, shugaban kungiyar hausawa mazauna Imo, Suleman Ibrahim Suleman, shugaban makiyaya na jihar, Yahaya Haruna da kuma masu rike da sarautun gargajiya na Obokofia.

A jawabin Ezeru kamar yadda ya fada wa mutanensa, bayan ganawar ta su ta kammala cewa yayi: “ Ina mai tabbatar maku da cewa na dau alqawarin isar da abinda muka tattauna zuwa ga mai girma gwamna, kasancewar mun tattauna abubuwa da dama.

“ Ina mai sanar da ku da cewa yanzu kowa ya kwantar da hankalinsa saboda bamu da wata barazana ta tsaro, an riga an dauki matakan da suka dace.”

Shi kuwa Suleman, shugaban hausawa cewa yayi: “ Ina neman gafararku bisa laifin da makiyayan nan suka aikata. Domin yafe laifin shi ne zai dawo mana da zaman lafiyan da muka saba yi.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel