Matasan Arewa za su gana da gwamnoni akan wa’adin da suka bada game da batun Ruga

Matasan Arewa za su gana da gwamnoni akan wa’adin da suka bada game da batun Ruga

-Gamayyar kungiyoyin arewa sun bayyana cewa za su gana da gwamnonin jihohin arewa don tattaunawa game da batun samar da Ruga

-Hakan ya biyo bayan da gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin jim kadan bayan da suka yi kira da a kaddamar da shirin

Gamayyar kungiyoyin arewa (CNG ) sun bayyana cewa za su gana da gwamnonin jihohin arewa don a tattauna game da batun samar da Ruga.

A ranar 3 ga watan Yuli 2019, kungiyar da take da matasa da dama daga yankin arewa, ta bayar da wa’adin kwana 30 ga shugaba Buhari da ya kaddamar da shirin samar da Ruga a duk fadin kasarnan. Amma sai gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin jim kadan bayan sun bayar da wa’adin.

Shugaban gamayyar kungiyoyin, AbdulAzeez Suleiman a ranar Alhamis 11 ga watan Yuli 2019 ya bayyana damuwarshi akan yadda shuwagabannin yankin kudu karkashin jagorancin gwamnoninsu suka ki amincewa da shirin da gan-gan suka kuma yi nasarar lalata shirin.

KARANTA WANNAN: An yanke ma wani direba mai shekara 21 hukuncin shekaru 4 a gidan yari kan satar adaidaita sahu

A jawabin da suka fitar ranar Alhamis din, kungiyar ta bayyana cewa gwamnonin kudu maso gabashin kasar nan basu kyauta ba da suka zabi mutanen da za su shiga garuruwansu.

Shugaban gayammayar kungiyoyin ya kuma yaba da irin yadda kungiyar gwamnonin arewa karkashin jagorancin gwamnan jihar Plateau Simon Lalong suka fahimci kiran da suka yi a matsayin wanda a kayi don kare hakkin yankin arewa .

A ranar Laraba, 10 ga watan Yuli 2019, Legit.ng ta ruwaito cewa kungiyar matasa kiristoci na kudancin Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kama matsan arewa da suka baiwa gwamnonin kudu wa’adin kwana 30 akan cewa sai sun karbi shirin samar da ruga.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel