Zamfara: Kotun zabe tayi watsi da karar da aka shigar kan zaben Mutawalle

Zamfara: Kotun zabe tayi watsi da karar da aka shigar kan zaben Mutawalle

Kotun zaben gwamnan jihar Zamfara a ranar Juma’a, 12 ga watan Yuli tayi watsi da karar da Alhaji Zyyanu Salisu na jam’iyyar Action Peoples Party (APP) ya shigar, inda yake kalubalantar zaben Gwamna Bello Mutawalle na PDP.

Justis atima Zeberu, ta yi watsi da karar, biyo bayan wani roko da lauyan mai karar, Mista Obed Agu da Farfesa Agbo Madaki suka yi.

Zeberu ta yi watsi da karar bayan lauyan INEC da PDP, sun nuna rashin adawa.

Mai shari’ar tayi watsi da karar mai lamba: EPT/ZM/GOV/2019.

NAN ta ruwaito cewa karar da Salisu ya shigar yana kalubalantar hukuncin hukumar INEC na ba Mutawalle takardar shaidar cin zabe kan cewa bai cancan tsayawa takarar zabe ba kan cewa bai yi karatu mai zurfi ba, kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin 1999 da dokar zaben 2010.

KU KARANTA KUMA: Atiku da PDP sun nemi dauki, sunce an far ma shaidu a hanyarsu na zuwa kotun zaben Shugaban kasa

Masu karar, sun yi rokon cewa kotun zabe ta kaddamar da cewa Mutawalle bai cancanci takarar zabe ba a zaben da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris, don neman kujerar gwamnan Zamfara.

Sun kuma bukaci kotun zaben tayi umurci INEC da ta sake gudanar da sabon zaben gwamna a jihar Zamfara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel