An yanke ma wani direba mai shekara 21 hukuncin shekaru 4 a gidan yari kan satar adaidaita sahu

An yanke ma wani direba mai shekara 21 hukuncin shekaru 4 a gidan yari kan satar adaidaita sahu

Wata kotun Jos da ked a zama a Kasuwan Nama, a ranar Juma’a, 12 ga watan Yuli ta yanke ma wani mutum mai suna Friday Longkes, hukuncin shekaru hudu a gidan yari kan laifin satan wani adaidaita sahu.

Mai shari’a a kotun, Mista Lawal Suleiman, ya yanke masa hukuncin bayan mai laifin ya amsa laifinsa ga tuhume-tuhume biyu da ake masa na cin amana da kuma yaudara sannan ya roki kotu da tayi masa rangwame.

Sai dai kuma, ya baayyana cewa wanda ake zargin yaki dawo da kudin barnar da yayi kamar yadda yayi alkawari sannan ya siyar da adaidaita ba tare da sanin mai shi ba sannan ya karkatar da kudin zuwa ga amfanin kanshi.

Gokwat ya bayyana cewa a lokacin binciken yan sanda, wanda ake zargin ya amshi bakin cewa ya aikata laifin.

KU KARANTA KUMA: Atiku da PDP sun nemi dauki, sunce an far ma shaidu a hanyarsu na zuwa kotun zaben Shugaban kasa

Dan sanda mai karar ya kara da cewa laifin ya saba ma sashi na 297a sannan kuma hukuncinsa na a karkashin sashi naa 307 na dokar jihar Plateau da ke arewacin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel