Yawan talakawan Najeriya ya karu daga miliyan 86 zuwa miliyan 98 cikin shekaru 10 – UNDP

Yawan talakawan Najeriya ya karu daga miliyan 86 zuwa miliyan 98 cikin shekaru 10 – UNDP

-Kungiyar majalisar dinkin duniya ta bayyana karuwar da aka samu ta talakawa a Najeriya a cikin shekaru goma

-Kungiyar ta bada wannan sanarwar ne jiya Alhamis a New York dake kasar Amurka

-Kamar yadda rahoton da suka fitar ya nuna an samu karuwar kusan 50% aka samu na talakawan daga 2007 zuwa 2017

Wani bincike da Global Multidimensional Poverty Index (MPI) ta yi, ya bayyana mana cewa mutanen dake fama da talauci a Najeriya yawansu karuwa yayi daga miliyan 86 zuwa mliyan 98 a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2017.

A wani rahoto da Kungiyar yin ayyukan cigaba na musamman ta Majalisar dinkin duniya wato UNDP ta fitar a New York ranar Alhamis, ta bayyana cewa yawan mutanen dake fama da talaucin ya karu ne kawai da kashi 50% cikin shekaru goma.

KU KARANTA:Zaben 2019: Yau Atiku zai gabatar da bidiyo matsayin shaida a kotu

Rahoton ya cigaba da bayani a kan wannan lamarin inda ya danganta talaucin da matakai daban-daban wadanda a iya cewa sune ummul-haba’isin talaucin.

A Najeriya, rahotanni sun nuna cewa kimanin kashi 50% na ‘yan Najeriya na fama da talauci. Rahoton ya sake fadin cewa adadin zai iya sabawa da abinda gwamnatocin jiha da na kananan hukumomi zasu iya bada wa.

Kamar yadda yake a cikin rahoto cewa: “ A Najeriya, duk da cewa yawan wadanda ke fama da talauci bai karu ba sama da kashi 50%, adadin masu fama da talaucin ya karu daga miliyan 86 zuwa miliyan 98 daga shekarar 2007 zuwa 2017."

Wannan rahoto da muka samu daga UNDP ya bayyana mana adadin talakawan da Najeriya take da su daga shekarar 2007 zuw 2017 wanda ya bamu shekaru goma kenan cif.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel