Atiku da PDP sun nemi dauki, sunce an far ma shaidu a hanyarsu na zuwa kotun zaben Shugaban kasa

Atiku da PDP sun nemi dauki, sunce an far ma shaidu a hanyarsu na zuwa kotun zaben Shugaban kasa

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta na Shugaban kasa a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar a ranar Juma’a, 12 ga watan Yuli, sun bayyana cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun far ma shaidunsu.

Jam’iyyar, wacce ta nemi dauki, tace shaidu na a hanyarsu na zuwa kotun zabn Shugaban kasa a lokacin da aka kai masu harin.

“Labarin da ke zuwa mana ya nuna cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun far ma shaidun da ya kamata su je bayar da shaida ga PDP a kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban kasa a yau,” inji PDP.

A wani dan gajeren jawabi, jam'iyyar tace Livy Uzoukwu, jagoran lauyoyin PDP da Atiku/Obi a kotun zaben, ya sanar da kotun cewa an kai wa shaidun hari a hanyarsu na zuwa kotun don bayar da shaida akan zambar zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Gwamna El-Rufai ya rantsar da sabbin kwamishinoni (hotuna)

Jam'iyyar tace a sakamakon haka, alkalin shari'an, Justis Mohammed Garba, ya dage sauraron karar zuwa ranar Litinin, 15 ga watan Yuli, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel