Wata mata ta gaya ma kotu cewa mijinta shaidan ya ke bautawa

Wata mata ta gaya ma kotu cewa mijinta shaidan ya ke bautawa

-Wata mata ta bayyana ma kotu cewa mijinta shaidan yake bauta ma wa kuma yana kokarin shanye mata jin

-Mijin na ta ya bayyana cewa ba gaskiya bane sa'annan ya kara da cewa matar ba ta ganin mutuncinshi a matsayinshi na mijinta

Wata mata mai suna Priscilla Ncube ta gaya ma kotu a kasar Zimbabwe cewa mijinta shaidani ne, ta kuma bayyana cewa mijin na kokarin saka ta cikin bautar shaidan.

Ncube ta bayyana cewa mijin nata mai suna Stephen Ncube da suke zaune tsawon shekaru 45 ya bayyana kanshi a matsayin mai bautar shaidan bayan da ya yi ikirarin cewa zai shanye jininta har sai ta mutu idan bata shiga cikin tsafin su na bautar shaidan ba.

Ta bayyana cewa mijin nata ya taba jan ta zuwa kauyensu inda yayi kokarin ya saka ta cikin bautar shaidan bayan da ya bata umurni cewa kada ta ci ko ta sha komi tsawon kwanaki dayawa sa’annan ya rinka yin tsubbace tsubbace a kanta cikin dare har lokacin da ta samu ta gudu gidan makwabta.

Da yake bayar da nashi jawabin Stephen ya bayyana cewa matar ba ta ganin mutuncinshi da girmanshi a matsayinshi na mijinta.

KARANTA WANNAN: Da dumi-dumi: Gwamna El-Rufai ya rantsar da sabbin kwamishinoni (hotuna)

Ya bayyana cewa "Matata Priscilla Ncube ba ta da kirki. Munyi aure fiye da shekara 45 kuma ta na yawan jifa na da zargin yin tsafi."

Ya kara da cewa “A duk lokacin da na yi kokarin kwabarta, ba ta saurare na sa’annan ta rinka zagi na ta na kira na da shaidani. Haka take yi mani tsawon shekaru da dama.”

Da alkalin kotun, Rachael Mukanga ya tuntubi matar ko ta na da wata shaida da za ta nuna ta tabbatar da cewa mijinta na bautar shaidan, sai ta ce “Saboda suna yawan fada mani cewa idan ban shiga cikinsu ba za su shanye jinina har sai na mutu.”

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel