Maigida, Uwargida da yayansu 5 sun mutu a sanadiyyar hayaki daya turnukesu

Maigida, Uwargida da yayansu 5 sun mutu a sanadiyyar hayaki daya turnukesu

Wasu iyalai da suka hada da Baba, Mama da yaransu 5 sun mutu duka a zuwa daya sakamakon hayakain na’urar samar da wutar lantarki watau Janareta da suka shaka bayan ya turnuke dakinsu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan lamari mai muni ya faru ne a rukunin gidaje na ‘Too Much Money’ dake garin Elele, cikin karamar hukumar Ikwerre ta jahar Ribas, a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli.

KU KARANTA: Kwararru kuma amintattu kadai zan nada ministoci a gwamnatina, Inji Buhari

Maigida, Uwargida da yayansu 5 sun mutu a sanadiyyar hayaki daya turnukesu

Iyalan da suka mutu
Source: Facebook

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jahar Ribas, Nnamdi Omoni ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labaru, inda yace bincike ya nuna mamatan sun mutu ne a sanadiyyar hayaki da suka shaka yayin da suke barci.

Amma Omoni basu kammala gudanar da bincike ba, inda yace zasu cigaba da bincike gawarwakin mamatan wanda a yanzu haka suna can a ajiyesu a dakin gawarwaki na babban asibitin garin Elele.

Shima wani makwabcin mamatan daya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace sun farka da safe amma sai suka tarar da gidan mamatan a garkame, da karfin tuwo suka balla kofar gida, shigarsu keda wuya suka tarar da gawarwakin.

A wani labarin kuma, wasu matasa dake zaune a unguwar Hayin Malam Bello cikin yankin Rigasa ta jahar Kaduna sun halaka mahaifinsu a lokacin daya shiga gida ya tarar dasu suna dambe da juna, duk kokarin da aka yin a rabasu ya ci tura.

Matasan wadanda yan gida daya ne, amma dakinsu daban daban sun yi ta dambe a cikin gidansu, har sai da mahaifinsu ya shigo ya tarar dasu da misalin bayan sallan Isha’I, ya yi ta yi musu magana su rabu sun ki rabuwa, kawai sai zuciyarsa ta buga, nan ya yanke jiki ya fadi matacce.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel