An gurfanar da yan Shi'a 38 a gaban kotu

An gurfanar da yan Shi'a 38 a gaban kotu

Hukumar yan sanda birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis ta gurfanar da yan kungiyar akida Shi'a 38 a kotuna daban-daban a unguwar Wuse dake Abuja.

Yayinda hukumar ta gurfanar da 10 a kotun majistaren Wuse Zone 2, an gudanar da sauran 28 a kotun majistare dake Wuse Zone 6.

Mambobin kungiyar Shi'an da aka gurfanar sun bayyanawa kotu cewa basu aikata laifin da ake tuhumarsu da shi ba.

Hukumar ta cajesu da laifin tayar da tarzoma, gudanar da taro ba bisa doka ba, cin zarafin al'umma da sauran su.

KU KARANTA: Buhari ya samu nasara, kotu ta yi watsi da karar masu tuhumar kwalin karatunsa

Yayinda ake sauraron karar, Alkalin yan Shi'an, I. A Ishaq ya bukaci kotun ta baiwa mabiyan Zakzakin beli. Ya janyo hankalin cewa 9 daga cikin wadanda aka gurfanar kananan yara ne.

Alkalin kotun majistaren Zone 6 ya bayar da belin yan Shi'an yayinda Alkalin kotun Zone 2 ya hana bali kuma ya bukaci hukumar yan sanda ta garkamesu a wani kebabben waje amma ba a cikin kurkukun yan sanda ba.

An dakatad da karan zuwa ranar 18 ga watan Yuli, 2019 domin cigaba da sauraron karar.

Mun kawo muku rahoton cewa Hukumar yan sanda ta sake garkame mabiyar akidar Shi'a 65 a sabuwar zanga-zanga da suka gudanar da matattarar ma'aikatun gwamnati dake birnin tarayya Abuja.

Mabiya El-Zakzaky sun koma zanga-zanga ne bayan batakashin da ya faru tsakaninsu da jami'an yan sanda a majalisar dokokin tarayya inda suka jikkata jami'an yan sanda da lalata motocin jama'a ranar Talata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel